1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Siriya sun sake dakarun Majalisar Dinkin Duniya

March 9, 2013

Gwamnatin kasar Jodan ta tabbatar da cewa an saki dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya

Filipino United Nations peacekeepers drive at the Kuneitra border crossing between Israel and Syria, in the Israeli occupied Golan Heights March 9, 2013. REUTERS/Baz Ratner (ISRAEL - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Hoto: REUTERS

Gwamnatin kasar Jodan ta tabbatar da cewa an saki dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, da aka yi garkuwa da su kwanaki uku da su ka gabata a kasar Siriya.

Kakakin gwamnatin kasar ta Jodan ya ce yanzu haka su na cikin kasar ta Jordan, abun da Majalisar ta Dinkin Duniya da jakadan Pilipin da ke Jodan duk su ka tabbatar.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi maraba da matakin sako dakarun 21 'yan kasar Pilipin.

Mayakan da ke neman kifar da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad na kasar ta Siriya ne, su ka kama dakarun masu aiki kan iyakar kasar da Isira'ila, sannan su ka ce, sun dauki matakan ne, domin kare lafiyar dakarun daga rikicin da ke faruwa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh