RSF ta kwace iko da garin Babanusa
November 14, 2025
Tuni dai aka fara nuna fargaba kan mokomar fararen hular da ke birnin Babanusa ,kan yiwuwar mayakan na RSF za su iya aikata irin aika-aiktar da suka tafka a birnin Al-Fasheer da ya fada hanunsu makwanni biyun da suka gabata.
Ibrahim Yaseen na kungiyar agaji ta kasa da kasa na daga cikin masu wannan fargabar:
"Wadannan mutane da ba a iya ja musu linzami da zarar sun ga sun yi nasarar shiga wani garin da ke hanun makiyansu, duk da alkawauran da jagororinsu ke yin a kare fararen hula da firsinonin yaki,ba mu da tabbas kan mazauna garin na Babanusah za su tsira daga kashe-kashen huce haushi da da mayakan na RSF suka yi kaurin suna''
Rundunar sojin gwamnati dai na ikirarin kai har- hare da jiragen yaki kan zzugar motocin yakin mayakan na RSF,hare-haren da ma'aikatan agaji ke cewa, galibi suna ritsawa da fararen hular da ke kokarin tserewa yakin.
Jaridar The Sudanese ta ruwaito cewa gwamnati ta gabatar da sharuɗɗa uku kafin ta amince da tsagaita wuta da suka hada da janye dakarun ‘yan tawayen RSF daga yankunan da suka mamaye, da tura ‘yan sanda a wuraren, da kuma kafa wata ƙungiya ta ƙasa da ƙasa da za ta rika sa ido kan aiwatar da tsagaita wutar wanda RSF ta amince da shi tun ranar 6 ga Nuwamba.