1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Syria sun shiga birnin Aleppo

Abdullahi Tanko Bala
November 29, 2024

Mayakan 'yan adawar Syria sun shiga cikin birnin Aleppo birni na biyu mafi girma a kasar, a karon farko cikin gomman shekaru a cewar masu fafatuka da kuma 'yan adawa

Sojojin 'yan tawaye a Syria
Sojojin 'yan tawaye a SyriaHoto: Omar Albam/AP/picture alliance

Rami Abdelrahman shugaban kungiyar sa ido don kare hakkin al'umma a Syria ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Jamus dpa cewa 'yan tawayen sun shiga cikin Aleppo karon farko tun shekarar 2016

A halin da ake ciki sojojin Syria sun fada a cikin wata sanarwa cewa rundunar sojin gwmnatin sun kwace iko da wasu muhimman wurare da aka sami tashin hankali kuma za su ci gaba da yaki har sai sun fatattaki 'yan tawayen.

Sojojin sun kuma zargi 'yan tawayen da yada labaran karya domin hargitsa al'umma.

Fadan ya tilasta wa mutane kusan 14,000 barin muhallansu a cewar Majalisar Dinkin Duniya.