Yanayin sanyin bana a nahiyar Turai ya karu
February 5, 2019Talla
Yanayin sanyi a nahiyar Turai a bana, ya yi kamarin da aka jima ba a ga irinsa ba, duba da yawan dusar kankarar da ake samu da kuma irin yadda ta haddasa tsaiko ga wasu harkoki da aka saba na yau da kullum.
Sai dai duk da wannan kamari da sanyi ya yi, wasu Jamusawa na amfani da lokacin don fita wuraren da ke da tsaunuka suna wasannin zamiyar kankara tare da 'ya'yansu a wani tsari na nishadi ta hanyar amfani da wannan yanayi.