Yanayin zamantakewa a Maiduguri sakamakon rashin tsaro
September 23, 2014Talla
Shugaban mabiya darikar katolika na gundumar Maiduguri da wasu jihohin arewa maso gabashin Najeriya, Bishop Oliver Dashe Doeme, ya nuna rashin gamsuwarsa dangane da yadda gwamnatin Najeriya ke tinkarar yaki da 'yan kungiyar nan ta Boko Haram.
Bishop Dashe ya ce jama'a na fama da matsaloli sosai domin da yawa sun rasu wasu sun rasa matsugunnensu kuma adadin yara marayu ya karu sosai sanan babu wani yunkurin da gwamnati ta yi na biyan bukatun wadannan mutane, ko da a gajeren lokaci ne ga shi kuma yanayin rayuwa na kara matse musu.
Bishop din ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Ahmed Salisu inda ya fara shaida masa halin da yanzu haka ake ciki a garin Maiduguri na jihar Borno.