1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yanayin zamantakewar Iyalai a Togo

May 16, 2013

Matan karkara masu ƙaramin ƙarfi waɗanda kuma su ka rasa mazajensu a ƙasar Togo kan yi ayyukan da ba safai aka san mata da su ba dan samun na kaiwa bakin salati, kamar dakon kayyayaki

TO GO WITH AFP STORY BY JUSTINE GERARDY Lemba women bring their own cooking utensils to a local gathering on January 28, 2012 in Gutu, 250 kms southeast of the capital Harare in Zimbabwe. Yarmulkes bob as voices rise into a sacred song carried from ancient Judea to the scenic fields of a far-flung southern African village that is home to a 'lost tribe' of Israel. The verses were brought in a DNA-proven journey to Zimbabwe where the Lemba live in Africanized pockets of Jewish traditions that are still passed down thousands of years after their ancestors left the Middle East. Tucked away deep in the countryside, the Lemba's strict social rules have more in common with norms in Tel Aviv than Harare: no pork is eaten, meat is ritually slaughtered, and all males are circumcized. AFP PHOTO / JEKESAI NJIKIZANA (Photo credit should read JEKESAI NJIKIZANA/AFP/GettyImages)
Hoto: AFP/Getty Images

Duk da cewa akwai ranaku na musammman da Majalisar Ɗinkin Duniya ke keɓewa domin tunawa da mata, har yanzu akwai matan da ke ci gaba da wahala a kasashen daban-daban na Nahiyar Afirka, wannan rahoton ya duba mana rayuwar wata mata mai gudanar da aikin dako a babbar kasuwar birnin Lome na kasar Togo

Mallama Essi Djade kenan yar kimanin shekaru 50 da haifuwa, ta ke bayyana irin matsalolin da ta ke cin karo da su a wajen gudanar da aikin na dako wacce ta ci gaba cewa, wasu mutane ba sa tausaya mana suna nuna hasalarsu a hili, suna furta muna miyagun kalamai na zagi, kai har birai su ke kiran mu wai ba zamu samu abin za mu ci ba.

Aikin dako aiki ne mai wahalar gaske a wajen maza ma ballantana mata kuma mallama Djade ta share aƙalla shekaru 15 ta na gudanar da wannnan aiki, to ko me ya tura ta ga shiga wannan aiki na doko?

"Talauci ne da fatara suka tilasta min shiga wannan aiki, kuma ina mai tabbatar maka da cewa ba daɗi sai wahala, ka diba ka gani a tsawan inin jiya dala 100 kawai na samu, ga shi kuma a yau zan sauka da dala 25r kawai, kai a gaskiya aiki ne mai tsananin wuya gashi kuma kayan da mu ke dauka su na da nauyin tsiya".

Hoto: picture alliance/africamediaonline

A samakon ƙuncin rayuwar da mallama Djade ta kasance a ciki, da kasancewar kuma mijinta ya jima da rasuwa haka ta ke faɗi tashin kula da 'ya 'yan ta marayu guda hudu.

"Wannan shi kawai ne aikin da zan iya yi domin ciyar da 'ya 'ya na in kuma samu abinda zan biya kuɗaɗan karatun su, idan kuma na ƙi yin wannan aiki ai sai shiga sata, ka ga saboda haka mu ke zuwa nan Lome muna gudanar da wannan aiki".

Babu wani taimako da ta ke samu haka ta ke ci gaba da tattara 'yan kuɗaɗan tana kula rayuwar iyalin ta, fatan ta shi ne kar ta kamu da rashin lafiya, inda kuma ta bada shaidar idan mai aikin dako ta kamu da rashin lafiya.

Essi Jade ta kara da cewa wani lokaci su na samun hatsarin ababan hawa musamman ma na 'yan Acaba, ba su kuma kulawa da su, wani sa'in su ken kama gaban su suna kuma zangin su.

Burkina Faso, OuagadougouHoto: picture-alliance/dpa

Mata da dama da ke wannan sana'ar ta dako irin su Essi Djade na da yawan gaske kuma su na yin sana'ar ce a cikin irin wannan mawuyacin halin kuma akasarinsu mazauna karkara ne da ke zuwa cikin birane su na gudanar da irin wannan aiki.

Mawallafi: Yusuf Abdoulaye
Edita: Umaru Aliyu