1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yancin jarida na tsaka mai wuya

Yusuf Bala Nayaya
April 25, 2018

Shugabanni na siyasa na yin babbar illa ga demokaradiya da aikin jarida a cewar kungiyar 'yan jarida Nagari na Kowa, Reporters Without Borders (RSF) a rahoton shekara-shekara.

Internationaler Tag der Pressefreiheit
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Gambarini

Babban abin da rahoton na 2018 ya yi kokarin nunawa dai na zama irin illar da ke tattare da nuna tsana ga 'yan jarida da 'yancin da suke da shi sakamaton kalamai irin na 'yan siyasa kamar yadda Christophe Deloire babban sakatare na kungiyar 'yan jarida Nagari na Kowa RSF ke cewa:

Babban abin da rahoto ya rufe da shi shi ne irin illar da kalaman kyamar 'yan jaridar ke gani ga 'yancin fadin albarkacin baki baki daya musamman irin yadda shugabannin na siyasa ke furta kalamai yadda suka ga dama, idan aka kalli duniya baki daya a Philippines shugaban kasa ne ke barazana ta kisa ga 'yan jarida, a Amirka shugaban kasa ya kira 'yan jarida "makiyan al'umma" a Indiya jam'iyyun siyasa ce ke goyon baya ta kafar sadarwar zamani a nuna kyamar 'yan jarida . Haka ma batun yake a kasashen Turai inda shugabannin na siyasa ke batanci ga 'yan jarida, abin da ka iya sare gwiwar 'yan jaridar koma ya kai su ga rasa rayukansu."

Hoto: picture-alliance/AP Photo

A cewar rahoton na RSF a shekarar ta bara an samu koma baya mafi muni kan fadin albarkacin baki, a watannin bayan nan an samu kisan 'yan jarida biyu batun da ya dauki hankali, a Sulobakiya dan jarida mai bincike an harbe shi a watan Fabrairu 2018, haka nan a Malta 'yar jarida mai fafutkar yaki da cin hanci da rashawa a shafin Blogg Daphne Caruana Galizia an halakata ta hanyar sa mata bam a mota a watan Oktoba 2017. A cewar Deloire babban sakataren na RSF wannan ba karamar barazana ba ce ga 'yanci na fadin albarkacin baki.

A Amirka dai da ke zama ta 45 kan jadawalin kasashen na duniya an ga karuwa ta lalacewar ga kame-kamen 'yan jarida lokacin zanga-zanga ko ma hana masu bayanai a cewar RSF Jamus na a mataki na 15.

Idan muka koma Afirka kuwa kudu da hamar Sahara rahoton ya ce yankin ya ci gaba da kasancewa a mataki na uku duba da kaso na nahiyoyi da dan samun ci gaba a shekarar ta 2017, saura da me idan aka leka daidaikun kasashen nan ne matsalar take. Misali a Najeriya da Mali idan suna aiki da ya shafi tsaro kamar yadda Arnaud Froger da ke jagorantar sashin Afika a kungiyar ta RSF.

Hoto: Getty Images/AFP/D. Faget

A Kamaru Ahmed Abba dan jarida ne da aka sako shi a watan Disamba 2017 bayan kwashe watanni 29. Ana kuma ganin yadda mahukunta ke kama karyarsu kan abin da ya shafi fadin albarkacin baki duba da katse hanyoyin sadarwar intanet a yankin da ke magana da Ingilishi.

A Côte d'Ivoire da ke a mataki na 82 mahukunta sun kama 'yan jarida takwas inda suka nemi su ba da bayanan inda suka samo labaransu bayan tawayen sojoji a 2017. Ba da rahoto dai da ya shafi mahukunta ya zama tashin hankali a kasashen na Afirka Nijar ta yi kasa da rasa matakai biyu inda take a mataki na 63 kama dan jaridar gidan talabijin Baba Alpha da aka kora zuwa iyakar Mali na zama misali. Senegal ta daga da mataki takwas inda take a mataki na 50 saboda batun da ya shafi dokar 'yanci ga 'yan jaridar. Malawi ta yi rawar gani saboda ba da damar samun bayanai. Kasashe irinsu Gambiya Zimbabuwe da Angola sauyin shugabanci ya samar masu da sabon fata. Kasar Norway dai ita ke a saman jadawalin na bana yayin da Koriya ta Arewa ke zama kurar baya a can kasa.