1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

030510 Pressefreiheit Deutschland Quellenschutz

May 3, 2010

Idan ana maganar ƙuntatawa 'yan jarida, sau da yawa an fi mayar da hankali kan ƙasashe kamar Rasha, China ko Iran. To amma wai shin yaya matsayin 'yancin watsa labaru yake a nan Jamus?

Hoto: picture-alliance/dpa

Kundin tsarin mulkin tarayyar Jamus ya tabbatar da 'yancin watsa labaru da bayyana ra'ayi. Sashe na biyar na kundin tsarin mulkin cewa yayi:

"Kowa na da 'yancin bayyana ra'ayinsa, ko da baki ko a rubuce ko a zane. Yana iya yaɗa labaru ko kuma samo su daga kafofin dake akwai, ba tare da matsala ba. An tabbatar da 'yancin yaɗa labaru ta gidajen rediyo da telebijin. Ba za a tace labaru ba."

Haƙiƙa ƙasashe da dama suna sha'awar yadda Jamus ke da jaridu iri daban daban da kuma dokar ƙasa da ta shafi kafofin yaɗa labaru. To sai dai duk da haka wasu na sukan wannan tsari. Alal misali ƙungiyar 'yan jarida ta duniya wato "Reporters Without Borders" ta yi nuni da ƙarancin kariya daga kafofin samun labaru. Ta ce 'yan jarida na fargabar cewa ba kullum ne ake samun sirri a hirarrakinsu da masu tsegunta musu labaru ba. Duk da cewa kariya ga kafofin samun labarun na da muhimmanci ga aikin jarida. Ƙungiyar ta yi ƙorafin cewa tun bayan hare haren ta'addancin ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001, an yi ta yiwa 'yan jarida shari'a kan zargin taimakawa a tona asirin ƙasa. Gwamnatoci na ƙoƙarin yin amfani da hanyoyin shari'a don samun sunayen waɗanda ke tseguntawa 'yan jarida da labaru.

Ministar shari'ar tarayyar Jamus Sabine Leutheusser-Schnarrenberger ta sanar da kafa wata doka wadda za ta kare 'yan jarida daga irin wannan mataki na lauyoyin gwamnati.

"Za mu ƙarfafa 'yancin 'yan jarida. Za mu inganta bawa 'yan jarida kariya. Kuma za mu tabbatar cewa ba a hukunta wani ɗan jarida akan laifin taimakawa a tona asirin ƙasa ba, idan amfani kaɗai yayi da bayanan da aka ba shi."

Ƙungiyoyin 'yan jarida sun yi maraba da hukuncin da kotun tsarin mulkin Jamus ta yanke a cikin watan Maris inda ta haramta dokar tara bayanai. Wannan hukuncin ya tilastawa kamfanonin sadarwa tara bayanai tsawon watanni shida game da buga wayoyi da saƙonnin Email da abokan hulɗar cinikinsu ke yi, domin sauƙaƙa aikin hukumomin shari'a. Duk da cewa an soke wannan doka, amma ƙungiyar 'yan jaridar ta duniya na fargabar cewa nan ba da jimawa ba ana iya gabatar da wasu dokoki makamantan tsohuwar dokar domin har yanzu ana amfani da ƙa'idojin tarayyar Turai.

Har yau abin da ke zama tushen 'yancin 'yan jarida a nan Jamus shi ne hukuncin kotun tsarin mulki a shekarar 1966 inda ta wanke mujallar Spiegel daga ƙararta da aka yi saboda buga wani rahoto game da sojoji da kuma ƙungiyar tsaro ta NATOa Jamus.

Yanzu haka dai Jamus na matsayi na 18 daga jerin ƙasashe 175 dake tabbatar da 'yancin faɗar albarkacin da ƙungiyar 'yan jaridu ta duniya ke fitawar a kowace shekara. Ƙasashen dake sahun farko sun haɗa da Denmark, Ireland da Finnand waɗanda ke sahun baya su ne Turkemenistan, Koriya Ta Arewa sai Eritriya.

Mawallafa: Monika Dittrich / Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi