1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yankin Igbo na son shugabanci

January 12, 2022

Jiga-jigan siyasar yankin Igbo a Najeriya, na kara fito da bukatarsu ta neman shugabancin kasar. Wannan dai wani abu ne mai kama da alamun gagarumin koma baya ga masu neman kafa kasar Biafra.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Ko waye zai gaji shugban Najeriya Muhammadu Buhari a 2023?Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Manyan 'yan siyasar yankin Igbo biyu ne dai, suka fito fili domin nuna bukatar neman jagorantar Najeriyar daga yankin Kudu maso Gabashin kasar cikin tsawon sa'o'i 48 da suka gabata. Hakan dai na dada nuna alamun raba gari a tsakanin matasan kungiyar IPOB ta 'yan awaren yankin da kuma masu siyasar da a baya suka dauki lokaci suna goya musu baya. Tsohon gwammna jihar Abia Orji Uzor Kalu ne dai ya bude kofar tuban, kafin daga baya gwamnan jihar Ebonyi kuma shugaban gwamnonin yankin Dave Umahi ya biyo baya a neman mulkin da ke nufin ci gaba a karatun hada kai na kasar. Umahin da ya gana da shugaban kasar dai ya ce ana iya shawo kan matsalar Biafran a siyasance, tare da bude tattaunawa da jagoran awaren da a yanzu ke hannun jami'an gwamnatin kasar. Umahin ya ce akwai bukatar bude tattaunawa da gwamnatin Najeriyar, domin samar da zaman lafiya a tsakanin al'ummar yankin. Koma ya take shirin kayawa a tsakanin masu siyasar da ke fadin tattaunawa da kuma matasan da ke kara yin nisa cikin dawa dai, gaza shawo kan matasan na tsakanin raunin dattawa ko kuma goyon bayan masu takama da siyasar yankin. Mohammed Sale Hassan dai na zaman jagoran kungiyar One Nigeria mai fafutukar hade kan kasar wuri guda, a cewarsa masu siyasar Kudu maso Gabas na shirin amsa tambayoyin gaza shawo kan tayar da kayar bayan matasan yankin da ke barazana ga makomar kasar. Abun jira a gani dai na zaman iya cika burin 'yan siyasar na Igbo, tare da fatalwar Biafra na binsu.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani