1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Luhansk da Donetsk na son shiga Rasha

Ramatu Garba Baba
September 20, 2022

Luhansk da Donetsk da suka bayyana ballewa daga Ukraine, sun tsunduma cikin shirin gudanar da zaben raba gardama don aminta kan shiga cikin tarayyar Rasha.

Ukraine Ausstellung von russischen Pässen in der Volksrepublik Lugansk
Hoto: Alexander Reka/dpa/TASS/picture alliance

A gaggauce mahukuntan na Luhansk da Donetsk suka sanar da shirinsu na gudanar da zaben raba gardama don cimma matsaya kan shiga cikin tarayyar Rasha, an shirya gudanar da zaben na ba-zata daga ranar Juma'a zuwa Lahadi da ke tafe in ji sanarwar da aka fitar a wannan Talata.

Yankunan biyu da a baya ke karkashin ikon Ukraine kafin su balle su zama masu cin gashin kansu da taimakon Mosko, sun tsinci kai cikin tsaka mai wuya a sakamakon nasarorin da Ukraine ke samu na sake kwace iko da wuraren da Rasha ta kwace tun bayan barkewar yakin na Turai. Ana ganin Rasha na kokarin sauya salon yakin ne don samun galaba kan makwabciyarta, ganin yadda ta amince da zaben da masana ke cewa, zai iya ba ta damar hada karfi wajen murkushe Ukraine.