1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKenya

'Yansanda na ci gaba da afka wa masu bore a Kenya

June 27, 2024

Ana ci gaba da arangama tsakanin jami'an 'yansanda da masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Kenya, duk da matakin janye dokar haraji da shugaban kasar ya yi.

Wasu masu zanga-zanga a Kenya
Wasu masu zanga-zanga a KenyaHoto: Daniel Irungu/EPA

Rahotannin da ke fitowa daga Nairobi babban birnin kasar Kenya, na cewa 'yansanda na can suna harbe-harben barkonon tsohuwa da harsasan roba a kan masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba William Ruto.

Masu boren dai sun sake karade manyan titunan kasar ta Kenya ne a yau Alhamis, duk da cewa shugaban kasar ya ba da umurnin janye karin harajin da ya haddasa tarzomar da ta kai ga mace-mace.

Matasan Kenya wadanda su ne galibi ke boren, sun ce ba za su janye ba saboda su ba su yarda Shugaba William Ruto zai iya kare masu makomarsu ba.

A shekaran jiya Talata ne dubban matasan suka kona majalisar dokoki, a daidai lokacin da 'yan majalisa suka amince da dokar karin haraji da Shugaba Ruto ya gabatar.