1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yansanda na cikin shirin ko-ta-kwana a Najeriya

Uwais Abubakar Idris M. Ahiwa
August 2, 2024

Yayin da aka shiga rana ta biyu ta zanga-zanga a Najeriya, Sufeta Janar na ‘yansandan kasar ya sanar da sanya jami'ansa cikin shirin ko-ta-kwana saboda barkewar rikigingimu da aka fuskanta a ranar farko ta zanga-zangar.

'Yansanda cikin shiri a Najeriya
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Tashe-tashen hankula da rikici da kwasar ganima da kisan mutane da aka yi a jihohin da ke arewacin Najeriya, ya sanya Sufeta Janar na ‘yansandan kasar Kayode Egbetokun bayyana fushinsa a kan cewa 'yansanda za su yi maganin dukkanin masu tayar da fitina, kuma tuni aka sanya su a cikin shirin-ko-ta kwana. 

A cewar Sufeta Janar na ‘yansandan Najeriyar, gungun zauna gari banza sun yi ta afka wa dukiyar jama'a tare da lalata ta, kuma manufar masu zanga-zangar ce su afka wa dukiyoyin jama'a, barnar da aka yi ta wuce iyaka a cewarsa inda ta shafi jihohin Kano da Kaduna da Borno da Yobe da jihar Neja da Bauchi da Gombe jihar Jigawa da ma Abuja. Don haka jami'an 'yansanda su shirya don dauka mataki mai tsanani kan duk wanda ya yi kokarin  kawo cikas ga bin doka da zaman lafiya.

A yini na biyu na zanga-zangar tsadar rayuwa, matasan sun sake fitowa a Abuja shelkwatar kasar inda jim kadan bayan da suka taru a unguwar Berger da ke birnin jami'an 'yansanda suka jefa musu hayaki mai shake numfashi inda suka watse. A garin Minna na jihar Neja, masu zanga-zangar ba su fito ba a Juma'ar nan inda harkoki suka koma daidai, inda rahotannin sun bayyana cewa an bude  kasuwami don ci gaba da harkoki.

'Yansanda da masu zanga-zanga a NajeriyaHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Haka lamarin yake a jihohin Nassarawa da Kogi da Kaduna inda aka dauki tsauraran matakan tsaro. A jihar Nassarawa, ana ci gaba da dokar hana fita a wasu kananan hukumomin jihar. A yayin da wasu jihohi kamar Lagos da Oyo aka samu masu zanga-zangar lumana.

A rana ta biyu an dan sassauta dokar hana fita a jihar Borno daga karfe 12 ranar zuwa karfe uku domin a bai wa Musulmai damar zuwa sallar Juma'a. Tuni dai masharhanta ke bayyana abin da ya kamata a yi bisa ga zanga-zangar da matasan suka dage sai sun kwashe kwanaki goma suna yi.

A daukacin jihohin kudu maso gabashin Najeriya dai ba a yi zanga-zangar ba. A kudu maso kudanci ma jihohi biyu ne aka ga fitowar jama'a. Duk da ja baya a yini na biyu na zanga-zangar, jami'an tsaro ba su ja da ba ya ba sanin abin da ya faru a zanga-zangar adawa da zargin 'yansanda da cin zarafin jama'a a 2021.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani