1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaBangladesh

'Yansanda sun koma aiki a Bangaladash bayan kyama

August 12, 2024

Bayanan da ke fitowa daga Bangaladash sun tabbatar da komawa aiki da jami'an tsaron kasar suka yi, bayan daidaita al'amura da sabon shugaban rikon kasar ya yi.

Dansandan kasar Bangaladash
Dansandan kasar BangaladashHoto: Luis Tato/AFP

'Yansanda a Dhaka babban birnin kasar Bangaladash sun koma aiki a yau Litinin, bayan janyewar mako guda ta biyo bayan zafin boren da ya kawo karshen mulkin shekaru 15 da tsohuwar firaministar kasar Sheikh Hasina ta yi.

'Yansandan na Bangaladash sun fuskanci tsananin kyama a musamman birnin na Dhaka da ke dauke da mutum miliyan 20, inda suka bayyana cewa ba za su yi aiki ba sai har an tabbatar musu da matakai na kare lafiyarsu lokacin aiki.

Kyamar dai ta biyo tsananin afka wa masu zanga-zanga da 'yansandan suka yi ne da ta kai ga kisan sama da mutum 450, ciki har da jami'an 'yansanda 45.

Tattaunawa da aka yi da shugaban wucin gadin kasar Muhammad Yunus ce ta kai ga dawo da 'yansanda a bakin aiki.