1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

María Corina ta lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya

Abdoulaye Mamane Amadou
October 10, 2025

Fitacciyar 'yar adawa a Venezuela, Maria Corina Machado, ta lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya ta bana, duk da kokarin da shugaba Donald Trump yake na fafutikar wanzar da zaman lafiya

María Corina Machado da ta lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya
María Corina Machado da ta lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya Hoto: Pedro Rances Mattey/Anadolu Agency/IMAGO

Jagorar 'yan adawar Venezuela, María Corina Machado ta lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya ta bana, duk da cewa tana rayuwa a boye. Kwamitin bayar da kautar ne ya kira madugar 'yan adawar mai shekaru 58 a duniya, tare da sanar da ita cewar ta cancanci kyautar ta bana, bisa kokarinta na fafutikar samar da dimukuradiyya

An nuna fifiko ga siyasa a kyautar Nobel ta bana - Fadar White House

Shugaban kwamitin Nobel a kasar Norway, Jorgen Watne Frydnes, ya bayyana Machado a matsayin jaruma, guda daga fitattun mutanen da ke zama abin misali a siyasance, da kuma ke aiki tukuru wanda ake gani a zahiri a yankin Latin Amurka.

A cikin jawabinta María Corina Machado ta ce "Ina ganin zai dauke ni dogon lokaci kafin in sake farfadowa daga abin da na ji a yanzu" a lokacin da aka sanar da ita ta wayar tarho da cewar ita ce ta lashe kyautar.

Masu yaki da makaman nukiliya sun lashe lambar yabo ta Nobel

"Wannan babbar daukaka ce, kuma na san wannan girmamawa ce ga mutanenmu ga al'ummar Venezuela baki daya," in ji María Corina Machado. A yanzu hakan dai fitacciar 'yar adawar na boye ne a wani wajen da ba san da shi ba, bisa matsin lambar da take fuskanta daga bangaren gwamnatin Venezuela da ke yi wa rayuwarta barazana.