1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKanada

'Yar bindiga ta bude wuta kan dalibai a Canada

February 11, 2026

Wata da ake zargin 'yar bindiga ce ta kashe mutane akalla 10 a wata makaranta da ke yankin British Columbia na Canada.

Motar 'yan sanda a wajen da aka kai hari a Canada
Motar 'yan sanda a wajen da aka kai hari a CanadaHoto: Andrej Ivanov/AFP/Getty Images

'Yan sandan Canada sun sanar da cewa baya ga mutanen da aka halaka a harabar makarantar Tumbler Ridge a British Columbia, an ga gawar wasu mutane biyu a rukunin gidajen da ke yankin, wanda kuma ake hasashen na da alaka da harin 'yan bindigar.

Karin bayani:Mutum na karshe na harin Kanada ya mutu

Kafofin yada labaran Canada sun rawaito cewa ana mace ce ta kai harin, wanda ba kasafai ake ganin mata da irin wannan mummunar dabi'a ba a yankin arewacin Amurka.

Karin bayani:Mutum 80 sun tsallake rijiya da baya a hadarin jirgin Canada

Firaministan Canada, Mark Carney, ya bayyana kaduwarsa kan wannan mummunan hari a Tumbler Ridge, tare kuma da aike wa da sakon ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda suka mutu, da kuma fatan waraka ga wadanda suka samu raunuka.