1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKamaru

'Yar Paul Biya na fuskantar kara bisa laifin tallata madigo

Mouhamadou Awal Balarabe
July 10, 2024

Wata kungiya ta kasar Kamaru da ke adawa da neman jinsi ta shigar da karar 'yar shugaban kasa Brenda Biya gaban wata kotun Yaoundé babban birni bisa zarginta da tallata luwadi da madigo a tsakanin al'umma.

Paul Biya bai ce komai game da badakalar madigo na 'yarsa Brenda ba
Paul Biya bai ce komai game da badakalar madigo na 'yarsa Brenda baHoto: Jemal Countess/UPI/newscom/picture alliance

Wannan matakin shigar da kara ya biyo bayan wallafa hotonta da abokiyar zamanta 'yar Brazil da Brenda Biya ta yi, inda suke sumbatar juna da nufin bayyana cewar su 'yan madigo ce. Duk da cewa Brenda Biya ta cire wannan hoto a shafinta na sada zumunta tare da bayyana cewar ta raba gari da 'yar Brazil mai nuna kayan kawa, amma tana ci gaba da shan caccaka daga wasu 'yan Kamaru yayin da 'yan LGBTQ ke nuna mata goyon baya.

Sai dai har yanzu shugaban kasa Paul Biya bai ce komai game da wannan batu ba. A Kamaru, neman jinsi ya haramta, kuma duk wanda aka samu da laifin luwadi ko madigo ko tunzura jama'a ga neman jinsi na iya fuskantar hukuncin daurin watanni shida zuwa shekaru biyar a gidan yari. Amma dai Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta yi tir da  cin zarafi da 'yan madigo da 'yan luwadi ke fama da su akai-akai a kasar Kamaru.