MDD: Hadarin kamuwa da kyanda ga yara
April 14, 2020Talla
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kananan yara kimanin miliyan 117 a fadin duniya na fuskantar hadarin kamuwa da cutar kyanda saboda kasashe da dama sun takaita allurar rigakafin cutar yayin da suka mayar da hankali ga yaki da annobar COVID 19.
Hukumarr lafiya ta duniya da asusun kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF sun ce a halin da ake ciki kasashe 24 da suka hada da wadanda ke fama da cutar kyanda sun dakatar da allurar rigakafin.
A shekarar 2018 mutane dubu 140 ne suka mutu a dalilin cutar kyanda yawancinsu kananan yara.
Musamman ana fama da cuatar ta kyanda a kasashen Bangaladesh da Brazil da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo da Sudan ta Kudu da Najeriya da Ukraine da kuma Kazakhstan