Yara da dama sun rasa rayukansu a Yemen
January 16, 2018UNICEF ta fitar da wannan rahoto ne a Sanaa babban birnin kasar a gaban manema labarai, inda ta ce yara kusan miliyan biyu basa zuwa makaranta, cikinsu rabin miliyan sun bar zuwa makaranta ne tun farkon rikicin kasar a watan Maris na 2015 daidai lokacin da rundinar sojojin da Saudiyya ke yi wa jagoranci ta soma kai hare-hare a kasar ta Yemen, sannan wasu yaran miliyan daya da dubu 800 ke cikin mawuyacin hali na tamowa.
UNICEF ta ce daga soma rikicin kawo yanzu an haifi yara fiye da miliyan uku, wadanda rayuwarsu ta kasance cikin hali na yaki, da gudun hijira, da cutuka da talauci da kuma karancin abinci. Rahoton Asusun kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya Unicef ya ce fiye da rabin 'yan kasar ta Yemen basa samun ruwan sha mai tsafta, inda cikin yaran da ke fama da matsalar tamowa, kusan yara dubu 400 ne ke bukatar a yi musu magani cikin gaggawa.