1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yara marayu fiye da 2000 ke son tallafi saboda Ebola

Yusuf BalaNovember 7, 2014

Kungiyar kawancen kasuwancin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ta bayyana cewa tallafin da kasashe zasu bayar a yaki da Ebola ya wuce batun magunguna.

Kinder in Sierra Leone
Hoto: UNICEF

Kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO ta ce cikin batutuwan da ya kamata a sanya idanu a kansu sun hadar da lura da yara marayu da dama, da mahaifansu suka rasu ta sanadin wannan annoba ta Ebola dama batun tattalin arzikin kasashen da wannan annoba ta shafa.

A cewar shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ta ECOWAS, ya ce tallafin kasashen yankin da ma na sauran kasashen duniya ya wuce batun kawai tallafawa fannin kawar da cutar ita kadai.

Fiye da yara marayu 2000 ne aka yi musu rijista a kasar Laberiya , kamar yadda bayanai suka nunar cikin wata takarda da taron na kungiyar ta ECOWAS ya fitar a birnin Accra na kasar Ghana.