1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yara na kwana a kan titunan Beirut sakamakon rikici

Mahmud Yaya Azare MAB
October 10, 2024

Unicef ya nuna damuwa kan mawuyacin halin rayuwa da yara kanana suka shiga a Lebanon, bayan da rikicin wata guda da Isra'ila ta kaddamar a kasar ya tilasta wa dubban mutane barin matsugunansu domin kwana a tituna.

Wasu yara sun shiga cikin mawuyacin hali tun bayan fara rikicin Isra'ila a Lebanon
Wasu yara sun shiga cikin mawuyacin hali tun bayan fara rikicin Isra'ila a LebanonHoto: Marwan Naamani/dpa/picture alliance

Hukumar lafiya ta Lebanon ta tabbatar da cewar daga cikin mutane kimanin dubu uku da hare-haren Isra'ila suka halaka a kasar har da yara kanana 1189. Ita ma Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta MDD ta ce hare haren wata guda na jiragen yakin Isra'ila kan Lebanon  sun raba aƙalla mutune miliyan 1.2 da muhallansu, almarin da ya sa dubban yara kwana a kan tituna.

Karin bayani:Sabbin hare-haren Isra'ila sun sa 'yan Lebanon tserewa

Sai dai kakakin asusun na Unicef a Lebanon Tess Ingram ya ce wajibi ne a gagauta samar wa yaran da ke watangaririrya a kan titiunan kasar musamman a birnin Beirut da  matsuguni mai mutunci. Ya ce: "Yara kanana 'yan Lebanon suna bukatar kwanciyar hankali da zaman lafiya, ba sake jefa su cikin tarzoma ba. Barin su suna watangaririya kan tituna bayan raba su da matsugunansu, keta huruminsu ne. Masu ruwa da tsaki kan ayyukan agaji na MDD su gaggauta samar musu da sansanin da za su rayu cikinsa, su yi barci cikin mutunci, a maimakon barinsu suna kwana kan titunan a birnin Beirut."

Karin bayani:Rikicin Israila da Hezbollah: Mene ne sirrin kemewar Iran

'Yan Lebanon na tserewa a duk lokacin da Isra'ila ta kai sabon farmaki ta samaHoto: Hussein Malla/AP Photo/picture alliance

Ummu-Rahma da 'y'ayanta shida ne ke kwance a titunan Beirut, kuma ta ce rikici ne ya tilasta musu kwana a kusa da bola. Tana fatan a kawo karshen yaki ko da ba za su samu damar komawa gidansu da aka yi raga-raga da shi ba. Ummu-Rahma ta ce: “Mun tsere daga gidanjanmu ba shiri, ba mu san yadda za mu fita ba. Mun ma taki sa'a, don mintuna biyar bayan ficewarmu ne hare-haren Isra'ila suka yi raga-raga da su. Da fari mun doshi sansanin 'yan gudun hijrara da aka ce mana an tanada, amma da muka isa sai muka tarar da shi ya cika makil ba masaar tsinke.”

Karin bayani:Hezbollah ta tabbatar da kashe Hassan Nasrallah

Kungiyoyin agaji na ci gaba da gina sansanoni don tarbar 'yan gudun hijira. Sai dai kamar yadda shugaban hukumar agaji ta Yasmeen da ke kasar Oman, Hasan Zahir ke cewa, muddin Isra,ila ba ta sassauta hare-haren da take kaiwa saman Beirut bisa zargin Iran da fasa kwabrin makamai  ba, dole ne za a ci gaba da samun tasgaro a ayyukan agaji da gina sabin sansanonin.

 Karin bayani:Fargabar ta'azzarar rikici bayan kisan Nasrallah

Netanjahu ya yi alkawarin lalata lebanon idan 'yan kasar ba su yi wa Hezbollah tawaye baHoto: OHAD ZWIGENBERG/AFP

A nasa bangaren, firaiministan Isra'ila ya mai da martini kan sukar da kungiyoyin agaji ke masa na kai hare hare kan unguwannin da ke dankare da fararen hula, ba tare da bayar da isasshen lokacin tserewa ba, inda Benjamin Netanyahu ya ce: "Hanya mafificiya ga 'ya'yanku kanana da garuruwanku sh ine, ku yi wa kungiyar Hezbollah tawaye, ku ba mu bayanan sirri don gaggauta kawo karshen jagororinta da rumbunan makamanta. Yin haka ne kawai zai hana ku fuskantar irin makomar Gaza.”