1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Macron ya gana da Yarima bin Salman

Ramatu Garba Baba
July 28, 2022

Shugaba Emmanuel Macron ya karbi bakunci Yarima Mohammed bin Salman a birnin Paris. Ziyarar ita ce ta farko da yariman ke yi tun bayan kisan dan jarida Jamal Khashoggi.

Saudi-Arabien | Besuch französischer Präsident Emmanuel Macron
Hoto: Saudi Press Agency/dpa/picture alliance

A wannan Alhamis Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya karbi bakunci Yarima Mohammed bin Salman na Saudiyya a birnin Paris. Ziyarar ta biyo bayan ganawa kai tsaye a tsakanin yariman da shugaban kasar Amirka Joe Biden a birnin Jidda na Saudiyya makonni biyu da suka gabata. Kafin Faransa yariman ya kai ziyara kasar Girka.

Ganawar yariman da Macron na zuwa ne duk da sukar da ake ci gaba da yi wa Yarima Salman, kan zarginsa da hannu a kisan dan jaridan nan Jamal Khashoggi. Akwai wani rahoto da hukumomin leken asirin Amirka suka fitar da ya tabbatar da cewa, Yarima Mohammed ne ya shirya sanadiyyar mutuwar Khashoggi, ko da yake masarautar Saudiyyar ta gaggauta musanta wannan zargin.  

Kisan fitaccen dan jaridan tare da daddatsa gawarsa da jami’an Saudiyya suka yi a karamin ofishin jakadancin kasar da ke birnin Santanbul na kasar Turkiyya a cikin watan Oktoban 2018 ya haifar da suka daga kasashen duniya.