1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yariman Saudi Arebiya ya bukaci kawo karshen yakin Gaza

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 11, 2024

Bin Salman ya bayyana Falasdinawa da 'yan Lebanon a matsayin 'yan uwansa da ke bukatar kariya daga hare-hare cikin hanzari.

Taron shugabannin kasashen musulmi
Hoto: Saudi Press Agency/dpa/picture alliance

Yarima mai jiran gado na kasar Saudi Arebiya Mohammed bin Salman ya yi kira ga kasashen duniya da su gaggauta daukar matakan kawo karshen yakin Gaza da kuma na Lebanon.

Karin bayani:Kasashe 52 na son MDD ta haramta wa Isra'ila sayen makamai

Mohammed bin Salman wanda ke jawabi a taron kungiyar hadin kan Larabawa ta Arab League da kuma ta hadin kan musulmin duniya OIC a birnin Riyadh na Saudi Arebiya, ya ce wajibi ne Isra'ila ta mutunta 'yancin gashin kai da Iran ke da shi, kuma ta kauce wa kai mata farmaki.

Karin bayani:Kasashen Larabwa da na musulmi sun bukaci gaggauta tsagaita wuta a Gaza

Haka zalika ya bayyana Falasdinawa da 'yan Lebanon a matsayin 'yan uwansa da ke bukatar kariya daga hare-hare cikin hanzari.