yarjejeniya tsakanin Majalisar Ɗinkin Dunia da DW
March 6, 2007Talla
Majalisar Dinkin Dunia da Redio DW, sun rataba hannu a kan yarjejniya, wace a sakamakon ta, DW za ta tallafawa Majalisar, wajen wayar da kan al´umma a game da al´ammura daban-daban na rayuwa.
Shugaban Redio DW, Errick Bettermann, da mataimakin Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia, Shashi Tharoor, sun bayyana cewar, ɓangarorin 2 sun yi na´am, da yin masanyar ra´ayoyi, da kuma ƙirƙiro sabin shirye-shirye.
A sakamakon wannan yarjejeniya,Gidan Talbajan na DW da ke da cibiyar sa, a birnin Berlin, zai ɓullo da saban shiri na moko-mako, wanda ya jiɓanci cuɗe-ni- in cuɗe ka, tsakanin ƙasashen dunia, sannan gidan Redio DW dake nan Birnin Bonn, zai maida hankali mussamman, wajen yaɗa shirye-shirye, zuwa nahiyar mu ta Afrika.