Iran: Ko yarjejeniya da Amurka za ta dore?
May 28, 2026
Barazanar ta shugaban Amurka Donald Trump kan fadada hare-harensa kan kasar Oman, wacce ke bai wa Iran hadin kai dangane da mallake iko da Mashigin Ruwan Hormuz na barazana ga yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran da dama take tangal-tangal.
Karin Bayani: Bukukuwan babbar sallah a Gabas Ta Tsakiya
Kafofin yada labaran Iran din sun yi ta nuna hotunan bidiyon harba gwamman rokoki da jirage marasa matuka, a kan wani sansanin jiragen saman Amurka a yankin da ba su fayyace ba. Harin na matsayin abun da suka kira ramuwar gayya kan hare-haren da Amurka ta kai a ranar Talata 26 ga watan Mayun 2026 a kusa da tashar jiragen ruwa ta Bandar Abbas da aka ce ba ta yi barna ba.
Yaki ka iya koma wa sabo?
Kakakin Rundunar Kare Juyin-Juya halin Musulunci ta Iran Ebrahim Zolfaghari ya ce, ba sa tsoron koma wa yakin muddin Amurkan ba za ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tsakaninsu ba. Bayan hare-haren ramuwar gayyar na Iran, rundunar sojojin kasar Kuwait ta sanar da harin makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki da aka kai wa kasar ba tare da bayar da bayyana daga ina harin ya fito ba.
Rundunar sojojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya ta ce, ta kai hari kudancin Iran da kuma kan wasu jiragen ruwan kasar da ke dasa nakiyoyi a karkashin teku. Mai magana da yawun rundunar ya ce, sun kai harin ne don yin kan-da-garkin barazanar da sojojinsu ke fuskanta daga wajen Iran. Sai dai ya ce, hakan ko kusa baya nufin kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wutar da suke ci gaba da mutuntawa.
Karin Bayani: Amurka na sa ran cimma yarjejeniya mai karko da Iran
Shi ma sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce duk da bai wa hamata iskar da aka samu tsakanin bangarorin biyu, yunkurin diplomasiyar da zai kai ga cimma yarjejeniyar kawo karshen yaki na ci gaba da kankakama. Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ba zai yi gaggawa wajen cimma yarjejeniya ba, musamman idan har hakan ba zai tabbatar da cewa za a bude Mashigin Ruwan Hormuz ba. Sabani kan Hormuz dai, na ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya da ma barazanar fadada yakin.
Oman cikin barazanar Trump
Trump ya yi barazanar ragargaza kasar Oman, muddin za ta ci gaba da bai wa Iran hadin kai a kokarinta na mallake iko da Mashigin Ruwan Hormuz din. Iran ta shelanta cewa, sabon daftarin da Amurka ta mika mata na fahimtar juna da za su rattaba hannu kansa, ya bai wa kasar ikon yin tasarrufi da mashigin ba tare da karbar kudin fito ba. To sai dai tuni Shugaba Trump din ya fito ya musanta wannan ikirarin, yana mai siffanta daftarin da Iran ke ikirarin ta karbe shi daga hanun masu shiga na Pakistan din da zallar tatsuniya.
Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar