Yarjejeniyar Amurka da Yuganda ya dauki hankali
August 22, 2025
"Daga Amurka zuwa Yuganda" wannan shi ne taken labarin da jaridar die Tageszeitung ta rubuta a kan yarjejeniyar korar bakin haure da tushensu 'yan gudun hijira ne a Yuganda. Kuma da haka ne muke yaye kallabin sharhunan jaridun na Jamus a kan Afirka.
Jaridar ta ce, bayan shafe makwanni ana tattaunawa a asirce, yanzu labari ya fara fitowa fili cewa gwamnatin Amurka karkashin Shugaba Donald Trump ta sanya hannu kan yarjejeniyar korar bakin da wasu kasashe, cikin su har da Yuganda. A nan gaba, gwamnatin Amurka na son yin jigilar bakin haure da masu neman mafaka wadanda aka debo su a kan iyakar Mexico da kuma zuwa sansanonin karbar 'yan gudun hijira da ke can, zuwa wata kasa ta uku kafin su iya neman mafaka a Amurka.
Karin Bayani: Sudan da rikicin Angola cikin Jaridun Jamus
Bisa labarin da jaridar ta samu, tawagogin Amurka da dama sun ziyarci Kampala babban birnin kasar Yuganda a makonnin da suka gabata. Shugaba Yoweri Museveni da kansa ya amince da yarjejeniyar, a cewar ma'aikatar 'yan gudun hijira, sai dai babu wani karin bayani daga bangaren ma'aikatar.
Shugaban Yuganda, wanda ya shahara a duk fadin nahiyar Afirka da al'adunsa na maraba da 'yan gudun hijira, ya gindaya sharudda; mutanen da za a tasa keyarsu zuwa Yuganda dole ne su kasance 'yan asalin Afirka kuma da radin kansu su amince a kai su Yuganda, kuma wajibi ne su kasance ba su da wani tarihin aikata laifuka.
Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung sharhi ta wallafa mai taken "Isra'ila na tunanin sake tsugunar da Falasdinawa a Sudan ta Kudu".
Jaridar ta ci gaba da cewar, bisa dukkan alamu dai Isra'ila na tattaunawa da gwamnatin Sudan ta Kudu domin ganin ko kasar za ta amince da daukar Falasdinawa daga zirin Gaza. Kamfanin dillancin labaran AP ya bayar da rahoton hakan, inda ya ambato majiyoyin kasashen biyu da kuma Masar. Sudan ta Kudu ita ce kasa mafi karancin shekaru, bayan samun 'yancin kai daga Sudan a shekara ta 2011 bayan yakin basasa na shekaru da dama. Yanzu dai kasar na gab da shiga wani sabon yakin basasa. Yana daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya, mai yawan mutane miliyan tara, wadanda kashi uku bisa hudu na su, ke dogaro da taimakon jin kai.
Halin da ake ciki a kasar bai hana gwamnatin Sudan ta Kudu mika kanta ga kasashen yammacin duniya a matsayin kasar da ke karbar bakin haure ba. A watan Yuli, wani jirgin sama dauke da mutane takwas da aka kora daga Amurka ya sauka a Juba. A bisa dukkan alamu gwamnatin Sudan ta Kudu na son cimma nasarar dage takunkumin da aka kakaba wa daya daga cikin jami'anta da kuma na hana wa 'yan kasar ta Sudan ta Kudu izinin shiga Amurka.
"Jiran zaman lafiya a Kinshasa-Kwango. Tattaunawar da aka yi tsakanin mayakan na M23 da gwamnati ta ci tura a halin yanzu" a cewar jaridar Welt Online.Kungiyar 'yan tawaye mafi girma a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, ta M23, ta janye daga tattaunawar sulhu da gwamnatin kasar. A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar 'yan tawayen ta ce za ta koma kan teburin tattaunawa ne kawai da zarar gwamnatin Kwango ta aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka amince da ita a baya.
Da farko dai ana sa ran bangarorin biyu za su rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Doha a farkon wannan makon. A watan Yuli ne aka cimma yarjejeniyar fahimtar juna ta hanyar shiga tsakani na kasar Katar. A wancan lokacin ma bangarorin biyu sun amince da tsagaita bude wuta. Duk da haka an ci gaba da gwabza fada.
Ana dai kallon yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kasashen biyu da ke makwabtaka da juna a matsayin wani sharadi na kawo karshen fadan. Gwamnatin Kwango da MDD da gwamnatocin kasashen yamma da dama sun sha zargin Ruwanda da goyon bayan mayakan M23. Duk da halartar tattaunawar zaman lafiya a Washington, Ruwanda ta yi watsi da wannan zargi.