1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU da Nija za su dakile safarar bil'Adama

Abdoulaye Mamane Amadou
July 16, 2022

Bayan shafe tsawon shekaru tana zama hanyar da bakin haure ke bi daga yammacin Afirka, jamhuriyar Nijar ta hada kai da kungiyar tarayyar Turai don magance matsalar.

Mahamadou Issoufou und Alexander De Croo
Hoto: Nicolas Maeterlinck/BELGA/dpa/picture alliance

Kungiyar Tarayyar Turai da Jamhuriyar Nijar na shirin hada karfi da karfe don yakar safarar bil'Adama da ke addabar nahiyoyin biyu.

Hukumar EU ta ce yarjejeniyar yaki da safarar bakin haure da ta kulla da Jamhuriyar Nijar ka iya taimakawa matuka wajen kakkabe 'yan baranda masu mummunar tabi'ar nan ta safarar bani Adama da jigilar bakin haure zuwa nahiyar Turai.

Tun da jimawa Jamhuriyar ta Nijar ke zama wata hanya tilo ta kwararar bakin haure daga kasashen yankin yammacin Afirka da dama, wadanda ke shiga Libiya da zummar zuwa Turai ta barauniyar hanya.