1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yakin Rasha da Ukraine na barazana ga aikin fitar da hatsi

Ramatu Garba Baba
May 17, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana fargaba kan barazanar da yarjejeniyar fitar da hatsi daga Ukraine ke fuskanta a sakamakon yakin gabashin Turai.

Kasashen Afirka da dama na dogaro da masarar Ukraine
Kasashen Afirka da dama na dogaro da masarar UkraineHoto: Olena Mykhaylova/Zoonar/picture alliance

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, tana kokarin ganin an tsawaita yarjejeniyar da ta cimma na fitar da hatsi daga Ukraine zuwa sassan duniya. Majalisar da ma masana sun baiyana fargaba kan halin ha-ula'i da kasashe musanman na nahiyar Afirka da Asiya ya zuwa Gabas ta Tsakiya za su fada ciki, muddun ba a tsawaita yarjejeniyar da a yanzu ke tanga-tangal ba saboda rincabewan yakin da ake ci gaba da gwabzawa a gabashin Turai.

Bayan barkewar yakin Rasha da Ukraine a watan Febrairun bara, aka soma fuskantar hauhawar farashin kayan hatsi a fadin duniya kafin daga bisani kasashen biyu da ke fada da juna tare da kasar Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya, su cimma matsaya kan rattaba hannu a wata yarjejeniyar da ta bai wa Ukraine damar fitar da kayan hatsi zuwa sauran kasashen duniya, wanda a baya, sojojin Rasha suka hana kasar yi a kokarin ganin sun kwace iko da kasar daga hannun Shugaba Volodymr Zelenskyy.