1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa kan fitar hatsi daga Ukraine

March 13, 2023

Majalisar Dinki Duniya da kuma Rasha sun fara tattaunawa kan sake sabunta yarjejeniyar fitar da hatsi daga Ukraine zuwa kasuwannin duniya.

Shugaban hukumar kula da ayyukan jinkai na MDD  Martin Griffiths
Hoto: Fabrice Coffrini/AFP

Yarjejeniyar fitar da hatsi daga Ukraine zuwa kasuwannin duniya a baya ya taimaka wajen rage matsalar karancin abinci da yakin Rasha da Ukraine ya haifar.

Bangaren wakilcin Rasha a Geneva ya tabbatar da cewa tuni tattaunawar ta fara gudana a tsakanin bangarorin biyu, sai dai kuma shugaban hukumar kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffith bai yi karin bayani kan tattaunawar ba ga manema labarai a lokacin da ya isa shalkwatar MDD da ke Geneva.

An dai ga yadda yarjejeniyar ta bayar da damar fitar da hatsi daga Ukraine ta takun Bahar Aswad a bara, inda alkalumma suka nuna an fitar da fiye da tan miliyan 24 na hatsi karkashin yarjejeniyar da MDD ta cimma da kasar Turkiya. A ranar 18 ga watan Maris din nan da muke ciki ne za a sabunta yarjejeniyar kai tsaye, face gwamnatocin Moscow da Kyiv sun ki amincewa.

Ko da yake fadar Kremlin ta yi ikrarin cewa ba a mutunta yarjejeniyar fitar kayan abinci da kuma taki daga Rasha ba. A ziyarar da ya kai birnin Kyiv a makon da ya gabata, sakataren MDD Antonio Guterres ya ce sabunta yarjejeniyar na da matukar mahimmanci.