Yarjejeniyar Isra'ila da Masar shekaru 40
September 17, 2018Jimmy Carter wanda tun lokacin da yake gwamnan Jihar Jojiya a shekara ta 1973 ya kai ziyara a Isra'ila inda ya samu damar yin wanka ruwan kogin yammacin Jordan wanda ake yi wa lakabi da ruwa mai tsarki da ke tsarkake wadanda suka yi imani da hakan. A lokacin ne ya ce bayan wankan sai aka cusa masa son 'yankin Gabas ta Tsakiya, inda daga bisani ya ce Ubangiji ya umarce shi da ya yi wani abu don sasanta rikicin Isra'ila da makobtanta. A karshe dai ranar 17 ga watan Satumban shekarar 1978, shugaban kasar Amirka na wancan lokacin Jimmy Carter ya samu damar hada taron marigayi shugaban kasar Masar Anwar Sadat da tsohon firamanistan Isr'ila na lokacin Menachim Begin, inda suka amince suka sa hannu kan jerjejeniyar zaman lafiya da hulda mai tarihi.
Anwar Sadat da Menachim Begin, kowannensu yana da cikakken darasi na illar mamayar kasa. Domin Sadat wanda aka haifa a shekara ta 1918, ya zo duniya ne lokacin da Birtaniya ta mamaye Masar. Sadat ya ba da misalin abin da ya faru shekaru shida kafin haifuwarsa inda wasu Misrawa kan kogin Nilu suka kashe wani sojan Birtaniya daya, daga nan sai Turawan mulkin mallaka suka kama 'yan kauyen 52 wasu aka rataye su wasu aka daure su a gidan yari. Don haka Anwar Sadat ya fadawa taron Camp David cewa al'ummar Masar bisa girman tarihinta da wayewar kanta kan tarihin duniya, ta fahimci tun tashin farko manufa da kuma ribar wannan yarjejeniyar.
Shi ma dai Firaministan Isra'ila na wacan lokacin Menachim Begin, ya fi kowa sanin illar mamaya, domin a shekara ta 1941 lokacin da 'yan Nazi suka mamaye kasar Belarus, sun kama kana suka Hallaka Yahudawa da yawa ciki har da iyayensa biyu. A lokacin da sojojin Nazi suka shiga, mahaifiyarsa na kwance a asibiti suka hallakata. Mahaifinsa na cikin Yahudawan da aka kama, aka jefe shi da duwazu bayan ya gama shan azaba suka jefa cikin ruwa. Don haka Menachim Begin yake alfahari da cewa shi Bayahude ne kuma zai sa hannu kan yarjejeniyar.
Wannan irin darasin da shugabannin Masar da na Isra'ila na wancan lokacin suke da shi kan illar yaki, ya yi matukar taimakawa wajen amincewarsu ga samar da zaman lafiya a taron na Camp David. Yayin da kafa kasar Isra'ila ya kasance dalilin rikin yankin Gabas ta Tsakiya, amma shugabannin biyu na ganin cewa a ci gaba da tashin hanakali babu wanda zai ci riba. Don haka suka yi gangamin samar wa kasashensu zaman lafiya. Domin a lokacin Isra'ila na ganin Larabawa 'yan ta'adda ne yayin da suma Larabawan ke daukar Yahudawan Isra'ila a matsayin tushen ta'addanci.
Don haka Sadat ya fada wa majalisar dokokin masar cewa shi ba wai amincewa da Isra'ila kawai ba, har majalisar dokokinsu zai je idan dai hakan zai hana daukar ran sojan Masar koda daya ne. Kuma ba da jimawa ba, a shekara ta 1977 Sadat ya kai ziyara Isra'ila inda ya yi jawabi gaban majalisar dokin Knesset. Wannan dai ya bata wa kasashen Laraba da dama rai, inda a lokacin kasashen Siriya, Iraki, libiya da Aljeriya suka yanke hulda da kasar Masar.
Duk da cewa shugabannin biyu sun samu kyautar zaman lafiya ta Nobel, amma ko da a cikin gida Anwar Sadat da Menachim Begin sun samu matsalar aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla. Hakan ta kai ga Shugaban Kasar Amirka Jimmy Carter ziyartar Isra'ila don kara mara wa firaministan baya daga Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi, yayin da Anwar Sadat lamarin ya kai ga masu tsattsauran ra'iyin sun harbe shi yayin wani Paretin soji. Kawo yanzu dai kasashen biyu na ci gaba da mutunta yarjejejniyar da aka cimma tun shekaru 40, domin a cikinsu ba wadda ke son ganin sojojinta sun shiga yaki da juna.