1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar Sudan biyu game da yankin Abyei

June 20, 2011

Hukumomin Khartum na Sudan da kuma na Juba ta Sudan ta kudu sun amince su kwance ɗamarar yaƙi domin kawo ƙarshen rikicin yankin Abyei da ke arzikin man fetur.

Sa hannu kan wata tsohuwar yarjejeniya tsakanin Sudan da kuma Sudan ta Kudu.Hoto: AP

Gwamnatin Sudan da kuma takwararta ta kudancin Sudan sun cimma yarjejniyar ƙwance ɗamarar yaƙi tsakaninsu a yankin Abyei mai arzikin man fetur da suke taƙaddama akai. Jami'in da ƙungiyar Gamayyar Afirka ta naɗa domin shiga tsakani, kana tsohon shugaban Afirka ta Kudu Thabo Mbeki ne ya bayyana wa kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya haka a birnin New-york bayan da ya tattauna da ɓangarorin biyu da ke gaba da juna. Mbeki ya ce wannan yarjejeniyar ta tanadi tsagaita buɗe wuta da kuma janye dakarun ɓangarorin biyu daga yankin da ba a kai ga yanke makomarsa ba.

Ita dai gwamnatin Sudan da ke da helkwatarta a birnin Khartoum ta girke sojojinta a yankin na Abyei da ke kan iyakarta da kudanci, bayan da ta zargi kudanci da kai wa sojojinta hari da ya hallaka wasu daga ciikinsu. Shi jami'in da ke shiga tsakani na Ƙungiyar Tarayyar Afirka ya nunar da cewar wannan yarjejniyar za ta iya share fagen kawo ƙarshen rikicin da sassa biyu ke fiskanta game da yankin kordofan ta kudu. Rikici da ake fiskanta tsakanin Sudan ta arewa da kuma ta kudu ya zo ne makwanni ƙalilan kafin ayyana kudancin Sudan a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas