1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Washington zata janje daga Afghanistan

Zainab Mohammed Abubakar
February 29, 2020

Washington da 'yan Taliban za su rattaba hannu kan yarjejeniyar da aka jima ana lalube, wanda kuma zai jagoranci Amirkan janye dubban sojojinta daga Afghanistan.

Afghanistan  Taliban Gefängnis
Hoto: picture-alliance/AP Photo/R. Gul

Shugaba Donald Trump na Amirka ya yi kira ga al'ummar Afghanistan da su bayar da damar samar da zaman lafiya a wannan kasa, bayan shekaru 18 na tashin hankula. Tun a jiya Jumma'a nedai Trump ya sanar da wakilcin sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo a wajen rattaba hannun na Qatar, a yayin da sakataren tsaro Mark Esper, zai gabatar da sanarwar hadin gwiwa da gwamnatin Kabul.

Ana saran yarjejeniyar kazalika, ta jagoranci daidaitawa tsakanin gwamnati da mayakan Taliban, wanda idan aka yi nasara, zai kawo karshen yakin da ya daidaita Aghanistan din na tsawon shekaru.