Yarjejeniyar sulhun Mozambik ta tashi aiki
October 22, 2013Da yammacin litini, babbar jami'yyar adawar Mozambik ta RENAMO ta ce ta yi watsi da yarjejeniyar sulhun da aka ƙulla a ƙasar a shekarar 1992, kuma wannan mataki na nufin cewa za ta ɗauki makamai ta koma gwagwarmaya da gwamnati da kuma jami'yyar da ke goyon bayanta wato FRELIMO. Yarjejeniyar ta shekaru 21 ta tashi aiki ne bayan da dakarun gwamnatin na Mozambik suka je suka anshe jagorancin babban sansanin 'yan ƙungiyar ta RENAMO,
ranar litini, dakarun gwamnati suka kai hari kan sansanin 'ya'yan RENAMO suka kuma anshe ta daga hanunsu. Na tsawon shekara guda ke nan shugaban RENAMO Afonso Dhlakama tare da ɗaruruwan dakarunsa masu makamai suka koma wannan sansanin da zama inda aka fi sani da Satunjira wanda ke cikin duwatsun Gorongosa a tsakiyar Mozambik. A lokacin yaƙin basasar ƙasar wanda ya afku tsakanin shekarun 1976 da 1992 an riƙa kiran wurin "Casa Banana" a turance. Wannan harin ya zo wa Afonso Dhlakama cikin bazata shi ya sa bai iya kaucewa ba amma kuma nan da nan ya mayar martanin cewa yarjejeniyar ta tashi, kamar yadda kakakin Renamo Fernendo Mazanga a shaidawa DW
Matsayin RENAMO
"Harin da gwamnati ta kai kan mazaunin shugaban jami'yya Afonso Dhlakama, tamkar ƙaddamar da yaƙi ne tunda ta yi amfani da dakarun soji. A daidai wannan lokaci, shugaban jami'yya Afonso Dhlakama na ƙoƙarin tsira da rayuwarsa ne domin kada dakarun si kai masa hari. Shi ya sa muke faɗawa duniya cewa, yarjejeniyar sulhun ta tashi aiki yanzu, abin da aka fara yanzu shi ne rikicin soji wanda muka so mu kaucewa tun farko
Tun bayan da aka yi bukin cika shekaru 20 da ƙulla wannan yarjejeniya a watan oktoban shekarar 2012, zaman tankiya ya daɗa ƙaruwa tsakanin manyan jami'yyun biyu. Ko a watan Afrilu mayaƙan RENAMO sun kai hari kan wani ofishin 'yan sanda a lardin Sofala, inda har mutane biyar suka hallaka, bacin haka kuma kun sake sun sake kashe wasu fararen hula biyu a wani harin da suka kai kan wata mota ƙirar Bus da kuma wani tantebur. Tun lokacin ne ya zamana sai ayarin motocin soji ne ke iya amfani da titin da ke haɗa kudanci da arewacin ƙasar.
Ra'ayoyin 'yan ƙasa
Ita dai RENAMO tana adawa da rinjayen da FRELIMO ke da shi a cibiyoyin gwamnati kuma tana neman a ƙara mata ƙarfin faɗa a ji a harkokin siyasar ƙasar. Rainer Tump wani bajamushe mai ba da shawarwari kan harkokin cigaba, ya kai ziyara sosai a ƙasar ta Mozambik kuma a ra'ayinsa, 'yan al'ummar da dama sun fahimci takaicin da RENAMO ke nunawa
"Kusan kowani furuci yanzu yakan fara da cewa abin da RENAMO ke yi ba shi da kyau, amma sun fahimci cewa abubuwan da gwamnati ke yi ne suka kaiwa RENAMO iya wuya, su kuma suka ce to yanzu tura ta kai bango. RENAMO ba ta ma sami damar yin maguɗi lokacin zaɓe ba, kuma da yawa sun goyi bayan haka, kuma a tunani na, shugaban ƙasar ma na da laifi sosai dangane da halin da kasar ta shiga yanzu
Yunƙurin FRELIMO na ayyana iko
Wani ɗan jaridar Mosambik mai suna Lui Lamarques na fasara harin da aka kai kan Afonso Dhlakama da muƙarrabansa a matsayin wani yunƙuri na FRELIMO, na ƙarfafa ikonta a ƙasar
"Idan har aka ga bayan Afonso Dhlakama tamkar an gurgunta RENAMO, saboda kuma ba da daɗewa ba za a koma kamar abin da ke faruwa a Angola, inda a can babu 'yancin walwala sosai. Duk jami'yyun da suka rage bayan an kawar da Dhlakama, ko kuma waɗanda aka ƙirƙiro, 'yan al'umma ƙalilan ne za su shiga, zasu kasance ne kaɗai domin su halatta zaɓuka su kuma taimakawa jamiyyar Frelimo wajen ayyana ikonta dindindin
Rikici tsakanin manyan jami'yyun biyu ya ƙara ta'azara ne a dalilin zaɓen ƙananan hukumomin da ake sa ran gudanarwa a watan Nuwamba idan Allah ya kai mu, bayan da RENAMO ta buƙaci hukumar zaɓe ta sanya wakilai daga manyan jamiyyun, shawarar da sauaran jamiyyun suka ƙi ansa, abin da ya sanyata yin barazanar ƙaurace wa zaɓen.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu