1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Kordofan a Sudan

August 23, 2011

Shugaba Omar al-Bashir ya bada sanarwar tsagaita wuta a yankin Kordofan mai arziƙin man fetur a wani mataki na sassanta rikicin

Shugaba Omar Hassan al-Bashir na SudanHoto: dapd

Shugaba Omar Hassan al-Bashir na Sudan ya bada sanarwar tsagaita wuta na makonni biyu a jihar kudancin Kordofan wadda ta fi arziƙin man fetur a ƙasar bayan da aka shafe makonni ana gumurzu tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye. Masu fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam sun zargi gwamnati a Khartoum da kai hari ta sama da ma wasu hare-hare akan ƙabilar Nubiyawa domin daƙile duk masu adawa da ita sakamakon ɓallewar kudancin Sudan. Tuni dai gwamnati a Khartoum ta ƙaryata wannan zargi tana ɗora alhakin akan ƙananan ƙungiyoyin ina da faɗa waɗanda suka yi faɗa da kudancin Sudan lokacin yaƙin basasar ƙasar. Shugaba Bashir ya ba da wannan sanarwar ne bayan da ya kai wata ziyarar bazata a jihar a wannan Talatar, a karon farko tun bayan da rikicin tsakanin dakarun gwamnatin da 'yan tawayen ya fara a farkon watan Yunin wannan shekarar. Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi zargin, kisar gilla, azabtarwa da cin zarafin fararen hula da kuma kwasar ganima a wasu daga cikin yankunan.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Mohammad Nasiru Awal