Yau ake zaɓen raba gardama a Kenya
August 4, 2010Yau ne al'umar Kenya ke kaɗa ƙuri'a akan sabon daftarin kundin tsarin mulki, da ka iya sauya manufofin wannan ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziƙi a gabashin Afirka. Wanan zaɓe na raba gardama dai ana ɗaukarsa tamkar muhimmin abin da zai hana sake aukwar tashe-tashen hankula da aka fuskanta, bayan zaɓen shekarar 2008, da ya kusa tsunduma ƙasar a cikin ruɗani mai ban tsoro. Ana sa rai cewa akasarin 'yan ƙasar ta Kenya za su kaɗa ƙuri'ar amincewa da daftarin kundin tsarin mulkin da ke neman kau da matsalar cin hanci da rashawa, daidata shugabanci na siyasa, warware gardamnar filayen ƙasa da kuma ƙabilanci da ƙasar ta Kenya ke fama da su tun bayan samun 'yancin kai a shekarar 1963. Kundin tsarin mulkin ya kuma gabatar da shawarar raba iko na shugaban ƙasa tare da ƙananan hukumomi, da kuma kare 'yancin al'uma.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu