Yau ICC za ta yanke hukunci game da yiwa Hissene Habre shari'a
July 20, 2012Talla
Harwayau, kotun za ta yanke hukunci ko ya kamata Mista Habre ya gurfana a ƙasar ta Senegal.
Ana zargin Mista Habre ne dai da laifin azabtarwa da kuma kisan dubun-dubatar masu adawa da shi lokacin da ya ke kan karagar mulkin ƙasar ta Chadi tsakanin shekara ta 1982 zuwa shekarar 1990 lokacin da soji su ka hamɓarar da shi daga karagar mulki.
A cikin shekara ta 2005 ne dai mahukuntan Belgium su ka shigar da ƙara gaban kotun bayan da wadanda gwamantin Mista Habren ta azabtar su ka gabatar da ƙorafinsu.
A yanzu haka dai tsohon shugaban yana zaman gudun hijira a ƙasar Senegal inda mahukuntan ƙasar ke masa ɗaurin talala.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Abdullahi Tanko Bala