Yau kwamitin sulhu zai kada kuri´a kan sanyawa Koriya Ta Arewa takunkumi
October 14, 2006Talla
Duk da cewa kwamitin sulhun MDD ya amince da kalaman da zai yi amfani da su cikin kudurin da zai tanadi sanyawa KTA takunkumi, rahotanni sun nunar da cewa kasashen Sin da Rasha ka iya nuna adawa da kudurin. A yau asabar aka shirya kada kauri´a a kan kakabawa gwamnatin Pyongyang takunkumi saboda gwaji makamin nukiliya da ta ce ta yi. A jiya juma´a jakadan Amira a MDD John Bolton ya gabatar da daftarin kudurin ga kwamitin sulhu. Daftarin kudurin bai tanadi sanyawa KTA takunkumin sayar mata da makamai ba to amma ya ba da umarnin gudanar da bincike akan kayakin dake shiga ko barin kasar mai bin tsarin kwaminisanci. A kuma halin da ake ciki wani jirgin saman Amirka na musamman ya gano birbishin wasu sinadarai a yankin tsibirin Koriya, wanda hakan ka iya tabbatar da ikirarin da KTA ta yi na yin gwajin makamin nukiliya.