Yau Merkel ke fara ziyarar aiki a Amirka inda zata gana da Bush
January 4, 2007Talla
A yau alhamis Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel zata gana da shugaban Amirka GWB a wata gajeriyar ziyara da take farawa yau a Amirka. Wannan ziyarar kuwa ita ce ta farko da Merkel zata kaiwa Amirka a matsayin ta na shugabar KTT da ta G-8 wato kungiyar kasashen masu arzikin masana´antu a duniya. Halin da ake ciki a yankin GTT na daga cikin muhiman batutuwan da shugabannin biyu zasu tattauna. Bugu da kari Merkel zata yi magana game da halin da ake ciki a Iraqi da Afghanistan sai kuma shirin nukiliyar Iran da aka kasa warwarewa. Jim kadan kafin ta tashi zuwa Washington SGJ ta goyi da bayan karfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin kungiyar EU da Amirka.