Yau take ranar dimokradiyya a Najeriya
May 29, 2017Talla
Akwai dai mabanbantan ra'ayoyi game da kamun ludayin shugaba Muhammadu Buhari kan muhimman batutuwa da suka hada da tsaro da tattalin arziki. Yayin da ake wannan biki na ranar ta dimokradiyya a gobe Talata kuma a kasar ake tuna shekaru 50 na masu fafutika ballewar Najeriya don kafa yankin Biafra, fafutikar da ta kai ga jefa kasar yanayi na yakin basasa, sai dai wannan lokaci na zuwa a daidai da lokacin da ake samun sabbin kiraye-kiraye na rajin kafa kasar ta Biafra inda 'yan fafutika daga Kungiyar (IPOB) da ta (MASSOB) ke kiran wannan rana a matsayin ranar tuna baya.