1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKamaru

Kamaru: Yaushe Biya zai sauka a mulki?

Zakari Sadou LMJ
October 27, 2025

An ayyana Shugaba Paul Biya ya sake lashe zaben shugabancin kasar Kamaru a wa'adi na takwas, na mulkin shekaru bakwai-bakwai.

Wannan na nufin Shugaba Paul Biya zai ci gaba da jan ragamar mulkin Kamaru na tsawon wasu shekaru bakwai, har zuwa shekara ta 2032. Ana dai ci gaba da zaman dar-dar a kasar, bayan da kotun tsarin mulkin zaben kasar ta ayyana Shugaba Biya a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da kaso 53.66 cikin 100 na kuri'in da aka kada da kuri'u sama da miliyan biyu.

Shi kuwa jagoran adawar kasar Issa Tchiroma Bakary ya samu kaso 35.19 cikin 100, wato sama da kuri'u miliyan daya ke nan. Tun bayan sanar da sakamakon, magoya bayan Tchiroma Bakary suka mamaye titunan kasar suna zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben, lamarin da ya kai ga jami'an tsaro amfani da karfi wajen tarwatsa masu boren da barkonon tsohuwa.

Zanga-zanga ce mafita?

Yamutsi a Kamaru bayan zaben Paul Biya a matsayin shugaban kasa karo na takwasHoto: Zohra Bensemra/REUTERS

Mazu zanga-zangar sun bankawa wani bangaren gidan shugaban karamar hukumar Douala biyu wuta, kana sun yi yukurin kona katafaren dakin taron karamar hukumar suka kuma kona gidan man Total mallakar Faransa duk a Douala. Matasa a halin yanzu na jiran alkawarin da shugaban ya yi musu yayin yakin neman zabe a Maroua, saboda galibinsu ba su da ayyukan yi.

A Yaounde babban birnin kasar kuwa mutane da dama sun fito kan titi kamar a Douala da Ngaoundere da Garoua da Maroua da kuma Bafoussam, suna kira ga Shugaba Biya ya sauka daga mulkin kasar abin ya ishesu haka. Sai dai sakamakon ya nuna al'ummar Kamaru mazauna Turai, sun zabi jagoran adawar kasar Tchiroma Bakary. Bakary ya samu kaso 62.79 cikin 100 na kuri'un 'yan kasar mazauna ketare, yayin da Biya ya samu kaso 22.63 cikin 100.

Ina makomar adawa?

Kimanin korafe-korafe 10 na zargin yin magudi a zaben na 12 ga watan Oktoba ne, majalisar kundin tsarin mulkin ta yi watsi da su. Gwamnatin Kamaru ta tabbatar da cewa mutane hudu ne suka rasa rayukansu a zanga-zangar da 'yan kasar suka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata a birnin Doula, gabanin sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a Litinin 27 ga wannan wata na Oktoba.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani