1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Yaushe za a sasanta da Orano?

Salissou Boukari LMJ
February 4, 2026

Ministan shari'a na Jamhuriyar Nijar Alio Daouda ya jagoranci girka wani kwamitin kwararru, wanda zai dukufa wajen tattara bayanai na tarin laifukan da kamfanin Orano na Faransa ya yi.

Nijar | Janar Abdourahamane Tiani | Rikici | Faransa | Uranium | Orano
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Jamhuriyar Nijar din dai ta ce, a wannan tafiya shure-shuren da kamfanin na Orano ke yi ba zai hana masa mutuwa kan wannan batu. Shi dai wannan kwamiti da ministan shari'a da kula da 'yancin dan Adam da hulda tsakanin manyan ma'aikatu na Nijar Alio Daouda ya kaddamar, ya kunshi kwararru a fannin shari'a da muhalli da kiwon lafiya da kare hakkin dan Adam da kuma masana hakar makamashin uranium. Kwamitin zai dukufa wajen tattaro bayanai domin samar da cikakken kundi da zai kunshi duk kararraki da sauran ja-in-ja da ke tsakanin Nijar din da kamfanin Orano na Faransa.

Zargin Orano ga Nijar

Akwai kamfanonin hakar ma'adinan uraniumu da Nijar ke da arzikinsaHoto: Joerg Boethling/IMAGO

Da yake magana kan zarge-zargen da kamfanin na Orano ke ci gaba da yi wa  Nijar, ministan shari'ar ya ce akwai abubuwa da dama da 'yan kasar da ma sauran al'ummar duniya ba su sani ba kan wannan batu.Tuni masu sharhi kan harkokin shari'a kamar Dakta Atto Namaiwa da ke bibiyar wannan ja-in-ja tsakanin Nijar da Orano sau da kafa ya ce, yana da kyau wannan kwamiti ya bi diddigin abubuwan da yarjejeniya tsakanin Orano da Nijar ta kunsa, domin gudun kar a yi kitso kai cike da kwarkwata.

Wane zargi Nijar ke wa Orano?

Nijar na da albarkatun kasa, ciki har da uranium mai yawaHoto: Maurice Ascani/Areva/AP Photo/picture alliance

A hannu guda kuma Nijar din ta zargi kamfanin na Orano da yin babban sakaci da ka'idojin kiyaye lafiya da muhalli, wanda a baya take cin karanta ba babbaka kan aikin na hakar uranium. Hukumomin na Nijar sun ce, sun bincika komai kuma ba su yarda da miyagun abubuwan da suka wakana tsawon shekaru ba. Kwamitin kwararrun, ya kunshi 'yan kungiyoyin farar hula masu kare hakin dan Adam da sauran masu sa ido kan albarkatun karkashin kasa da Nijar din ke hakowa.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani