1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Yancin fadin albarkacin bakiMali

AES: Yaushe 'yan jarida za su samu 'yanci?

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 6, 2026

Rahotanni daga Mali na nuni da cewa, an cafke wani dan jarida Youssouf Sissoko da ya yi fice wajen yin suka ga gwamnatin juyin mulkin sojan kasar.

Mali | Shugaban Kasa | Assimi Goïta
Shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Mali Assimi GoïtaHoto: AP/dpa/picture alliance

Kungiyar 'yan jaridu ta kasar Mali ta sanar da cewa, an cafke dan jarida Youssouf Sissoko da ke zaman manajan kula da sashen buga labarai na jaridar L'Alternance, bayan buga wani labari da ya soki shugaban gwamnatin mulkin sojan makwabciyar kasa Jamhuriyar Nijar.

Rahoton ya bayyana cewa Shugaba Janar Abdourrahamane Tiani ya yi jawabi "bisa yanayin da yake ciki", bayan da ya dora alhakin harin da aka kai a filin jiragin saman kasarsa a makon da ya gabata a kan kasashen Faransa da Côte d'Ivoire da kuma Benin. Da ma dai kamewa tare da garkame 'yan jarida ba bakon abu ba ne a kasashen Afirka, musamman ma na AES da suka hadar da Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso, kasashen kuma da ke fama da hare-haren 'yan ta'adda.