1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceGabas ta Tsakiya

Gaza: 'Yan jarida na ci gaba da halaka

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 25, 2025

Rahotanni daga yankin Zirin Gaza na Falasdinu, na nuni da cewa wasu 'yan jarida hudu na daga cikin mutane takwas din da suka hadu da ajalinsu a harin sojojin Isra'ila na asbitin Nasser da ke tsakiyar birnin Gaza.

Isra'ila | Hari | Asibiti | Nasser | Khan Younis 2025 | 'Yan Jarida | Kisa
'Yan jarida na cikin hadari a yankin Zirin Gaza na FalasdinuHoto: Stringer/REUTERS

Daga cikin 'yan jaridar da harin na Isra'ila ya halaka, har da Mariam Dagga da ke aiki da kamfanin dillancin labarai na Associated Press. Mai shekaru 33 a duniya, Dagga ce ta ruwaito labarin yadda likitoci a asibitin na Nasser ke fafutukar ceto rayuwar kananan yaran Zirin Gaza da yunwa ke nemana halaka su. Gidan talabijin din Al Jazeera ma ya tabbatar da rasuwar wakilinsa Mohammed Salam a wannan harin.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce, dan jaridarsa Hussam al-Masri ya halaka yayin da harin ya raunata dan jaridar Reuters din mai daukar hoto Hatem Khaled. Rundunar tsaron Isra'ilan IDF ta tabbatar da harin da ta kai a asibitin na Nasser da ke Khan Younis, tare da bayyana cewa ta yi da na sanin raunin da duk wani wanda bai-ji ba bai-gani ba ya samu kuma ba ta kai harin da nufin halaka 'yan jarida ba. Yakin Isra'la da Hamas dai, na zaman guda cikin wadanda suka fi lakume rayukan 'yan jarida, inda kawo yanzu 'yan jaridar 192 ne suka halaka a yankin Zirin Gaza na Falasdinu a yakin watanni 22.