Najeriya: Shin za a magance cin-hanci?
July 21, 2026
Bincike ne a tsanake kuma na lokaci mai tsawo da Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa a Ma'aikatun Gwamnati ta Najeriya ICPC ta gudanar, inda ta samu nasarar bankado kasurgumar satar da jami'an gwamnati suka dauki lokaci mai tsawo suna tafkawa ta hanyar cusa ma'aikata na bogi.
Har da na lahira ake biya albashi?
Wasu daga ma'aikatan da ake cusawa sun mutu wasu sun yi ritaya wasu kuma babu su, amma aka dinga karbar kudi da sunasu wasu mutanen dabam na zubawa aljihu. Tsabar kudi har Naira miliyan 942 ne, suka dinga zurarewa ta hanyar ma'aikatan bogi.
Wannan adadi da hukumar ta samo katse hanzarin sace su ne ta samu nasara a kotu, bayan da ta shigar da kara a kan wadannan ma'aikatu. Bankado yadda wadannan makudan kudi ke zurarewa ya faru ne, a daidai lokacin da kasar ke koken rashin isassun kudin gudanar da harkokin gwamnati.
Tsarin albashin bai-daya bai taimaka ba
Kasar ce dai ta 142, a rahoton Transparency International na 2025. Duk da bullo da tsarin biyan albashi na bai-daya da Najeriyar ta fara amfani da shi a 2007, domin kamanta gaskiya a ma'aikatun gwamnati amma masu halin bera na sauya salo da dabarun kaucewa wadannan matakai. Wannan ya sa kungiyar CISLAC ta bayyana da abin kunya, na gazawar daukar matakai na sadidan.