Yaushe rikicin 'yan bindiga zai kare a Filato?
July 9, 2025
Masana harkokin tsaro a Najeriya sun kawo shawara cewa, ya kamata gwamnatin Filato ta horas da jami'an tsaro 'yan sa-kai wato Vigilante domin su rika taimakawa wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar jihar Filato. Wannan na zuwa ne yayin da ake ci-gaba da fuskantar hare haren 'yan bindiga da ke aukuwa a wasu yankunan jihar.
Jihar Filato dai ta sha fama da rigingimu na kabilanci da addini, lamarin da ke janyo hasarar rayuka da dukiyoyin al'umma, Dangane da haka nema ake ci gaba da samun shigar matasa cikin kungiyoyi sa-kai domin taimakawa wajen magance wadannan nan rigingimu. Ko shin me ya sa aka kasa magance wannan matsala ta jihar Filato.
Tashin hankali na baya bayan dai shi ne wanda ya auku a tsakanin kauyukan Kukawa da Bunyum, da ke karamar hukumar Kanem, kuma rahotanni sun nunar da cewa an rasa rayukan mutane da dama yayin arangama tsakanin 'yan kungiyar sa-kai ta vigilante na yankin.
Yanzu haka ma dai matasa da ke karamar hukumar Wase wanda ke mawkabtaka da Kanem suma sun himmatu kokarin kare yankinsu daga 'yan bindigar kasancewar a lokuta da dama mazauna kauyukan Wase na fuskantar munanen hare hare daga 'yan bindigar.
Rundunar da ke wanzar da zaman lafiya a jihar Filato ta yi karin haske kan lamarin inda cikin sanarwar da ta fitar ta hanun Kakakin ta Major Samson Nantip, ta ce mutane 8 ne aka kashe a fito na fito tsakanin 'yan bindiga da 'yan sa-kai a yankin Kanem, amma ba mutane 70 ba kamar yadda wasu kafofin labarai ke bayyanawa.