1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Yaushe za a magance cin-zarafin mata?

Zakari Sadou LMJ
June 24, 2026

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta yi tir da cin-zarafin mata a Kamaru, inda ta zargi gwamnati da gaza yin katabus wajen yakar cin-zarafin mata a kasar da ke karuwa a kullum.

Kamaru | Cin-zarafi | Mata | Human Rights Watch
Gangamin yaki da cin-zarafin mata a KamaruHoto: Elisabeth Asen/DW

Rahoton da Human Rights Watch ta fitar ya ce, duk da alkawarin da mahukuntan Kamaru suka yi a shekara ta 2011 na dakile wannan matsala har yanzu abin kara habaka yake yi musamman bangaren yadda mazaje ke gallazawa matansu na aure ko 'yan mata abokan zamansu. Wata kididdiga da hukumomin Kamaru suka fitar ta nunar da cewa, mata 77 abokan zamansu suka kashe a shekarar 2024.

Mata su bayyana cin-zarafin da aka yi musu

Sai dai Human Rights Watch ta ce, alkaluman sun zarce haka kasancewar ba dukkan mace-macen ake kai rahoton afkuwarsu ba. Yayin wani taron tattaunawa kan matsalar cin zarafin mata karkashin jagorancin minista mai kula da inganta rayuwar mata da iyali Marie Therese Ondoua Abena da na sadarwa kana kakakin gwamnati Rene Emmanuel Sadi sun ce, ya kamata a dauki matakan da za su kawo karshen kashe-kashen mata.

Sai dai sun ce, ya kamata matan da suke fuskantar cin-zarafin su bayyana halin da suke ciki domin a dauki mataki kafin wani mumman abu ya faru.

Matasan Kamaru na fafutukar kawo sauyi a siyasar kasar

02:58

This browser does not support the video element.

Rahoton ya dogara ne kan binciken da aka gudanar tsakanin watan Satumba zuwa Disamba na shekara ta 2024, a biranen Maroua Yankin Arewa Mai Nisa da Douala yankin gabar teku Littoral da Buéa Yankin Kudu maso Yamma.

Rahoton ya tattara shaidu mata 60 da suka fuskanci cin-zarafi da tashin hankali, tare da yin wata tattaunawa da  jami'an gwamnati da kuma shugabannin addinai domin fahimtar girman matsalar da hanyoyin magance ta. Kungiyar ta nuna cewa, har yanzu akwai al'adu da dabi'un zamantakewa da ke halatta tare da ci gaba da karfafa cin-zarafi da tashin hankalin da ake yi wa mata.

Cin-hanci da rashawa na taka rawa

A cewar alkaluman hukuma a shekarar 2018 kaso 44 cikin 100 na 'yan mata da mata 'yan Kamaru masu shekaru tsakanin 15 zuwa 49 da ke rayuwa ko kuma suka taba rayuwa tare da abokin zama sun bayyana cewa, sun fuskanci cin-zarafi na tunani da jiki ko fyade daga hannun abokan zamansu.

Rahoton ya kuma nuna cewa, matsalar na kara ta'azzara ne saboda rashin horo da karancin kayan aiki ga jami'an da ke da alhakin kare wadanda abin ya shafa da kuma zargin cin-hanci da rashawa a cikin rundunar 'yan sanda da wasu hukumomin gwamnati.

Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani