1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Kwango: Yaushe za a rabu da annobar Ebola?

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 9, 2026

Rahotanni daga Jamhuriyyar Dimukuradiyyar Kwango na nuni da cewa, an sake samun rahoton bullar annobar Ebola a wasu sassan kasar da a baya suka yi fama da cutar.

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | Ebola | Asarar Rayuka
Ebola na ci gaba da yin ta'adi a Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Gradel Muyisa Mumbere/REUTERS

Mahukuntan Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ne suka tabbatar da hakan, a daidai lokacin da yawan wadanda suka halaka sakamakon kwayar cutar ta Ebola da aka samu a baya-bayan nan a kasar ya kai 600. A cewar ma'aikatar lafiya ta Kwangon, an samu rahotonnin alamomin sake bullar cutar a wasu Larduna biyu na kasar.

Wannan dai, na nuni da yadda cutar ke yaduwa fiye da lardin da ke zaman tungarta wato Ituri. Koda yake ma'aikatar lafiyar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon ba ta bayyana adadin wadanda ake zargin sun kamu da cutar a lardunan biyu ba, sai dai kawo yanzu alkaluma sun nuna adadin wadanda suka kamu da cutar Ebola a kasar ya kai 1,759.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW