'Yan awaren Abzinawa a Mali tare da kawayensu masu alaka da kungiyar Al-Qaeda, sun kai hari kan ayarin motocin dakarun gwamnati da mayakan Rasha na Africa Corps a arewacin kasar.
Shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Mali Assimi GoïtaHoto: ORTM/REUTERS
Talla
Kungiyar Azawad Liberation Front ta ce mayakanta sun kai harin ne a kusa da Tabankort, yayin da ayarin ke kan hanyarsa ta kai dauki ga sansanin sojoji da ke garin Anefis. Wata majiya ta tsaro a Malin ta tabbatar da cewa an yi wa ayarin kwanton bauna, kuma an ci gaba da gwabza fada.
'Yan Mali za su gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a ranar 12 ga watan Agusta a cikin mawuyacin halin tsaro, shekaru shida bayan fara fuskantar matsalar tsaro daga Abzinawa 'yan tawaye a arewacin kasar.
Hoto: picture-alliance/dpa
2012-2018 : Lokacin rikicin tsaro a Mali
A ranar 22 ga Maris na 2012 ne sojoji suka kwace mulki daga hannun gwamnatin Amadou Toumani Touré (da ke kan hoto), bisa zarginsa da "kasa daukar matakan da suka dace" don yakar 'yan tawaye da masu kaifin kishin Islama a arewacin kasar. Amadou Sanogo ne ya dare kan kujerar mulki.
Hoto: picture alliance/AP Photo/P. Nangia
Faransa ta taimaka da soji karkashin "Serval"
A ranar 11 ga Janairun 2013, Faransa ta yi amfani da karfin wuta, tare da hadin gwiwar kungiyar ECOWAS karkashin tsarin "Serval", a kan masu fafutuka da sunan Islama a arewacin Mali. An maye gurbin wannan tsari a 2014 da rundunar Barkhane, da zummar murkushe 'yan yakin jihadi da ke bazuwa a yankin Sahel.
Hoto: Reuters/B. Tessier
Harin kunar bakin wake na farko a kasar
A ranar 8 Faburairu na 2013, harin kunar bakin wake na farko na tarihin Mali ya auku a Gao da ke arewacin kasar, a kan sojoji. Kungiyar Mouvement pour l'unicité du jihad en Afrique de l'Ouest (Mujao) ce ta dauki alhakin harin. A daidai wannan lokaci a Bamako, sojoji suka kai farmaki kan sansanin tsaffin dakarun soji.
Hoto: Reuters
Kaddamar da rundunar tsaron Minusma
Rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali (Minusma), an kaddamar da ita a ranar 1 ga Yuli 2013 a hukumance. Ta maye gurbin rundunar kiyaye zaman lafiya ta Afirka da nufin taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a cikin kasar, tare da taimakon sojoji da 'yan sanda na Majalisar Dinkin Duniya guda 12.600.
Hoto: picture alliance/dpa/M. Kappeler
Ibrahim Boubacar Keita: Sabon shugaba
A ranar 4 ga watan Satumba 2013, Ibrahim Boubacar Keita ya lashe zaben shugaban kasa gaban abokin hamayyarsa Soumaïla Cissé. Sakamako ya nunar da cewar ya samu kashi 77,61% na kuri'un da aka kada. Manyan matsalolin da za a magance sun hada da tsaro da zaman lafiya da kalubalen zamantakewa.
Hoto: picture alliance/dpa
Jamus ta taimaka wa Mali
Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita ya gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a Berlin a ranar 11 ga watan Disemba 2013 da nufin karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Hoto: picture-alliance/dpa
2015, shekarar kashe-kashe da yawa
A ranar 7 ga watan Agusta 2015, mutane 13 sun mutu a lokacin rikicin garkuwa a otal din Byblos a Sévaré, da ke tsakiyar Mali. Ranar 20 ga watan Nuwamba kuma, wani hari da aka kai a otal Radisson Blu ya yi sanadin mutuwar mutane 20 a Bamako. 'Yan watanni kafin wannan, a Maris 2015, an kai wa gidan cin abinci na La Terrasse hari a babban birni, wanda ya kashe mutane biyar.
Hoto: S. Rieussec/AFP/Getty Images
Sulhu tsakanin gwamnati da 'yan tawaye
An sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a ranar 15 ga watan Mayu a Bamako tsakanin gwamnatin Mali da kungiyoyin tawaye karkashin sa idon kasa da kasa. Sai dai daga bisani, tashin hankali tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga da suka sa hannu kan yarjejeniyar ya yi barazana ga zaman lafiya a yankin Kidal.
Hoto: F. Batiche/AFP/Getty Images
Shari'ar Sanogo, shugaban mulkin soja
Shari'ar tsohon shugaban mulkin soja Amadou Haya Sanogo, wanda ya yi juyin mulki a 2012, ta fara a ranar 30 ga watan Nuwamba 2016 a Sikasso. Bayan kama su a Nuwamba 2013, Amadou Haya Sanogo da sauran wadanda ake tuhuma na da damar kare kansu daga zargin kisan dagorai 21 da ke kare lafiyar shugaban kasa.
Hoto: picture-alliance/dpa
Karuwar tashin hankali a arewacin Mali
A ranar 18 ga watan Janairun 2017, wani harin kunar bakin wake da kungiyar Al-Mourabitoune da ke da alaka da Aqmi ta kai, ya salwantar da rayukan mutane fiye da 70 a wani barikin soji na Gao da ke arewa maso gabashin Mali. A ranar Lahadi 22 ga watan Janairu, sojoji uku sun mutu bayan da wata mota ta taka nakiya tsakanin Gao da Timbuktu. A cikin kasa da mako daya, an kai wa Mali hari so biyu.
Hoto: Getty Images/AFP
Masu zanga-zanga na kira ga adalci a zabe 2018
A ranar 8 ga watan Juni 2018, mutane da dama sun gudanar da zanga-zanga a Bamako, don bayyana bukatar gudanar da sahihin zabe a Mali. Bisa ga kiran adawa da 'yan farar hula, masu zanga-zanga sun tada jijiyoyin wuya a karkashin kulawar jami'an tsaro da suka nuna dattaku bayan amfani da karfi da suka yi a zanga-zangar farko.
Hoto: AFP/M. Cattani
Macron ya tattauna batun tsaro da shugabannin G5-Sahel
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya halarci taron kolin shugabannin kasashen Afirka na AU da ya gudana a Nouakchott na Moritaniya, bayan wani sabon harin da aka kai kan sojojin rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta G5 Sahel a birnin Gao na Mali. Tare da shugabannin kasashe biyar da abin ya shafa, Macron ya tattauna matsalolin tsaro a yankin..
Hoto: picture-alliance/L.Marin
'Yan takara biyu da za su fafata a zagaye na biyu na zaben Mali
A yanzu dai za a gudanar da zagaye na biyu na zaben ne tsakanin Ibrahim Boubacar Keita da madagun 'yan adawa Soumaila Cisse a ranar 12 ga watan Agusta 2018. A shekara ta 2013 ma dai 'yan takarar biyu ne suka fafata a zagaye na biyu a zaben shugaban kasar Malin, inda shugaba mai ci Ibrahim Boubacar Keita ya samu nasara a kan madagun 'yan adawar Soumaila Cisse.
Hotuna 131 | 13
Kungiyar FLA ta kuma yi ikirarin kwace iko da garin Anefis, duk da cewa mayakan Africa Corps da wasu sojojin Mali na ci gaba da rike sansanin sojojin da ke garin. Tun bayan juyin mulkin shekarun 2020 da 2021, gwamnatin mulkin sojan Mali na ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro duk da alkawarin da ta dauka na dawo da zaman lafiya a kasar.