Sudan: Yaushe za a samu zaman lafiya?
April 15, 2026
Tun daga ranar 15 ga watan Afrilun 2023, Sudan ta fada cikin rikici mai tsanani tsakanin bangarori biyu masu karfi. Rikici tsakanin rundunar sojan kasar, karkashin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma RSF karkashin Mohammed Hamdan Daglo wanda aka fi sani da Hemeti. Shekaru uku kenan da fara rikicin, amma har yanzu babu wata alama ta kawo karshensa.
Yakin ya rutsa da mutane da dama
Alkaluman lissafin da Majalisar Dinkin Duniya na nuni da cewa, kimanin mutane miliyan 14 yakin na shekaru uku ya tilastawa yin kaura. Daga cikinsu sama da miliyan tara na hijira a cikin kasar, yayin da wasu kimanin miliyan shida ke gudun hijira a ketare musamman Chadi da Sudan ta Kudu da Habasha cikin halin ni 'yasu.
A birnin Khartoum da sauran yankuna, gine-gine sun lalace asibitoci sun daina aiki yayin da yunwa da cututtuka ke kara bazuwa. A yankin Darfur ma, ana fuskantar sabon tashin hankali mai kama da na baya. Duk da yunkurin sasanci daga kasashe da kungiyoyi na duniya ciki har da Amurka da Saudiya da Majalisar Dinkin Duniya, babu wata yarjejeniya mai dorewa da aka cimma.
Tsagaita wuta ta gaza amfani
An sha cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, amma sai ta rushe cikin kankanin lokaci. Hakan ya sa al'umma ke kara rasa fata, yayin da duniya ke ci gaba da kira da a kawo karshen wannan rikici. Yayin da ake cika shekaru uku na wannan rikici, tambaya ita ce: Yaushe ne za a kawo karshensa, kuma wa zai dauki alhakin wahalhalun da al'ummar Sudan ke ciki?