1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaushe za a tsagaita wuta a Gaza?

Abdul-raheem Hassan
September 10, 2024

Ma'aikatar tsaron kasar Isra'ila ta ce kofa a bude take na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na wucin gadi da kungiyar Hamas. Matakin zai iya samar da musanyar mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza inji Isra'ila.

Faladsinawa 14 sun mutu a sabon harin Isra'ila
Hoto: Hani Alshaer/Anadolu/picture alliance

Da yake magana da manema labarai, ministan harkokin tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya ce akwai haske kan cimma tsagaita bude wuta na tsawon makonni shida, har ma yuwar sako 'yan Isra'ila da a ke tsare da su a zirin Gaza tare da samar da zaman lafiya a yankunan da ke kusa da arewacin kasar Lebanon.

Ministan ya kara da cewa, Isra'ila ba za ta yi alkawarin kawo karshen luguden wuta a Gaza na din-din-din ba, kamar yadda kungiyar Hamas ta gindaya a sharudan yarjejeniyar.

Jami'an agaji a Khan Younis sun ce dakarun isra'ila sun yi barin wuta a tuddan na tsira da ke zirin Gaza, wanda ya kashe mutane akalla 40 wasu 60 sun jikkata.