Najeriya: Yawaitar muggan makamai
November 26, 2020La'akari da wani binciken Majalisar Dinkin Duniya tare da hadin gwiwar wani kwamiti da fadar shugaban kasar ta kafa tun shekarar 2009, 'yan majalisun Tarayyar Najeriya sun tabbatar da cewar, kimanin adadin makamai miliyan 350 daga adadin miliyan 500 da ke a nahiyar Afrika ta yamma na cikin Najeriyar. Hukumomin kasar dai sun bayyana cewar, faruwar hakan bai rasa nasaba da muggan ayyuka da ake aikatawa a sassa dabam-dabam na kasar da suka hadar da fashi da makami da satar mutane domin karbar fansa da yanzu ya zama ruwan dare da kuma tayar da kayar bayan kungiyoyi irin na Boko Haram da na asiri da ma 'yan Niger Delta da kuma 'yan bangar siyasa.
Karin Bayani: Kokarin shawo kan matsalar tsaro a Najeriya
Mr Nsofor Stanley jami'in wani kamfanin tsaro ne mai zaman kansa na Bull Shark Security a kasar: "Yanayin hakan na sa masu zuba jari barin kasar, sannan kasar na kan murmurewa daga annobar COVID-19, amma kuma kwatsam sai kasar ta sake fadawa sabon matsin tattalin arziki. A gaskiya kuma tsananin da jama'a ke fuskanta yanzu, zai dada gaba ne matsawar makamai na hannayen jama'ar da doka ba ta sahale musu ba, domin za su yi amfani da su ne ta hanyar da ba ta dace ba. Wannan koma baya ne ga kasar, sannan hakan na nufin ba wanda ke da tsaro a cikinmu."
Ana dai ganin gazawar jami'an tsaro a Najeriya a kokarin ganowa tare da tsare masu dauke da makamai ba tare da doka ta ba su dama ba, shi ne sanadin kwararar makamai a arewacin kasar da ya dade cikin gararin masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da kuma 'yan tayar da zaune tsaye da kan yi wa kauyuka dirar mikiya, su kashe mutane su kuma yi wa mata ko na aure ko 'yan mata fyade, sannan kuma su kwashi dukiyoyi.
Karin Bayani: Kara yawan makamai ga jami'an tsaron Najeriya
Rundunar 'yan sandan Najeriya dai, ta sha bayyana matakin karbe haramtattaun makamai da ke hannun mutane a kasar, amma matakin na karewa a fatar baki kawai. Fargabar da jama'a ke dada shiga na yanayin farmaki da wasu dauke da makamai kan kai, ya fara sanya tunanin cewar kowa ya dau matakin mallakar makamai domin kare kansa. Hada-hadar makamai dai a nahiyar Afrika tare da fataucin su, garari ne da aka nunar bai tsaya a nahiyar ta Afrika kadai ba har ya kai ga wasu nahiyoyin. Tarihin bayyanar makamai dai a kasar ya faro ne tun kafin mulkin Turawan mulkin mallaka, wato yayin hada-hadar bayi, inda Turawa su kai ta amfani da karfin bunduga domin ratsawa yankuna na Afrika da dama.